Tinubu ya nada Baguda a matsayin Shugaban Asibitin lafiyar Kwakwalwa da ke Kware-Sokoto.
Tinubu ya nada Baguda a matsayin Shugaban Asibitin lafiyar Kwakwalwa da ke Kware-Sokoto
Nadi
Daga Habibu Harisu
Sokoto, Nuwamba 26, 2025 (NAN) Shugaban kasa Bola Tinubu ya tabbatar da nadin Dr Suleiman Baguda a matsayin babban darektan kiwon lafiya / babban jami’in kula da asibitin lafiyar kwakwalwa na tarayya da ke Kware a jihar Sokoto.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan gudanarwa na asibitin, Alhaji Abdullahi Gada ya sanya wa hannu, kuma aka mika wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ranar Talata a Sokoto.
Gada ya ce an sanar da hakan ne ta hannun karamin ministan lafiya, Dr Adekunle Salako, inda ya kara da cewa ya kasance nadin na farko na shekaru hudu daga ranar 14 ga Nuwamba, 2025.
Kafin nadin Baguda, Cikkaken Likitan Kwakwalwa ya kasance mukaddashin Daraktan Asibitin, wanda ya kware a fannin ilimin tabin hankali daga Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) da Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) da Guru da Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, tare da wasu kwararru da horarwa.
Gada ya nuna jin dadinsa da karramawar da shugaban kasar ya yi masa, inda ya kara da cewa al’ummar asibitin sun yi maraba da wannan ci gaban da aka samu tare da yi wa daraktan lafiya fatan samun nasara. (NAN) (www. nannews.ng)
HMH/BRM

