Rashin Tsaro: Tinubu ya dage tafiya zuwa taron G20, AU-EU

Rashin Tsaro: Tinubu ya dage tafiya zuwa taron G20, AU-EU

Spread the love

Rashin Tsaro: Tinubu ya dage tafiya zuwa taron G20, AU-E

Tsaro

By Muhyideen Jimoh

Abuja, Nuwamba 20 2025 (NAN) Shugaban kasa Bola Tinubu ya dage ziyarar da ya kamata ya yi zuwa Afirka ta Kudu da Angola, yayin da yake jiran karin bayani kan tsaro akan ‘yan matan makarantar Kebbi da aka yi garkuwa da su da kuma harin da aka kai kan masu ibada a Eruku, jihar Kwara.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Mista Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya kuma ba da umarnin aikewa da karin jami’an tsaro zuwa kananan hukumomin Eruku da Ekiti na jihar Kwara.

Ya umurci ‘yan sanda da su bi sahun ‘yan bindigan da suka kai hari a cocin Christ Apostolic Church, Eruku.

Kanfanin Dillancin na Najeriya (NAN) ya tuna cewa a ranar Laraba ne shugaban zai tashi daga Abuja domin halartar taron shugabannin kasashen G20 da za a yi a Johannesburg, daga bisani kuma a taron AU da EU a Luanda.

Sai dai Onanuga ya ce Tinubu ya dakatar da tafiyar sa ne saboda tabarbarewar tsaro a Kebbi da kuma harin da aka kai a Kwara.

Shugaban ya kuma na dakon rahoto daga mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, wanda ya ziyarci jihar Kebbi a madadin sa, da kuma jami’an tsaro da ke bincike kan harin da aka kai a Kwara.

Tinubu ya nanata umarninsa ga hukumomin tsaro na ganin an sako ‘yan matan 24 da aka sace tare da tabbatar da komawarsu gida lafiya. (NAN)

MUYI/CHOM
===

Chioma Ugboma ta gyara

 

 


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *