Tinubu ya dage dokar ta-baci a Rivers, Fubara ya koma matsayin gwamna ranar Alhamis
Tinubu ya dage dokar ta-baci a Rivers, Fubara ya koma matsayin gwamna ranar Alhamis
Fubara
Daga Muhyideen Jimoh
Abuja, Satumba 19, 2025 (NAN) Shugaban kasa Bola Tinubu ya janye dokar ta-baci a jihar Ribas, kuma ya umurci Gwamna
Siminalayi Fubara da mataimakinsa da ‘yan majalisar dokokin jihar su koma bakin aiki.
A wata sanarwa da shugaban ya fitar a Abuja, ya ce matakin ya biyo bayan dawo da zaman lafiya da kwanciyar
hankali a jihar.
Ya ce “don haka, ina matukar farin cikin sanar da cewa dokar ta-baci a Ribas za ta kawo karshe daga tsakar daren yau.
“Gwamnan, Mai girma Siminalayi Fubara, mataimakin gwamna, Ngozi Nma Odu, da ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas da kakakin majalisar, Martins Amaewhule, za su ci gaba da aiki a ofisoshinsu daga ranar 18 ga Satumba.”
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa an kafa dokar ta-bacin ne a ranar 18 ga watan Maris a daidai lokacin da rikicin siyasa da kuma tabarbarewar harkokin mulki ta barke.
Cikin kwanciyar hankali, Tinubu ya jaddada mahimmancin komawa ga mulkin dimokuradiyya da daidaiton hukumomi a Rivers.
Shi dai babban jami’in da Tinubu ya nada, mataimakin Admiral Ibok-Ette Ibas mai ritaya, wanda ya jagoranci jihar tun a watan Maris, ya shirya ficewar ne tare da taron godiya ga mabiya addinai daban-daban da aka gudanar a ranar Lahadi a Fatakwal.
(NAN)(www.nannews.ng)
MUYI/SH
========
Sadiya Hamza ce ta gyara