Hukumar NSCDC ta kama wanda ake zargi da damfarar mace N1.8m
Hukumar NSCDC ta kama wanda ake zargi da damfarar mace N1.8m
Damfara
Daga Ramatu Garba
Kano, Satumba 4, 2025 (NAN) Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC) a jihar Kano, ta ce ta kama wani matashi
dan shekara 28 (an sakaya sunansa) bisa zargin damfarar wata mata Naira miliyan 1.8.
Kakakin rundunar, Ibrahim Idris-Abdullahi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Kano.
Ya ce wanda ake zargin dan asalin karamar hukumar Garko ne, kuma mazaunin unguwar Kawo a cikin birnin Kano, ana zarginsa da yi matw alkawarin karya na inganta ilimi da kasuwanci mai riba.
“Wanda ake zargin ya yi amfani da laya wajen yaudarar wata matar aure, inda ta raba ta da kudin da a samu sama da Naira miliyan daya da Dubu dari takwas,” inji shi.
Idris-Abdullahi ya ce rundunar ta kammala bincike kan lamarin, inda ya ce za a dauki matakin da ya dace a kan wanda ake zargin.
Ya kuma jaddada aniyar kare jama’a daga masu damfara da sauran miyagun ayyuka a jihar. (NAN)(www.nannews.ng)
RG/RSA
=======
Rabiu Sani-Ali ne ya gyara