Ministar harkokin mata ta yaba da hukuncin daurin shekaru 21 da aka yanke wa wanda ya yi wa yar wata uku fyade

Ministar harkokin mata ta yaba da hukuncin daurin shekaru 21 da aka yanke wa wanda ya yi wa yar wata uku fyade

Spread the love

Ministar harkokin mata ta yaba da hukuncin daurin shekaru 21 da aka yanke wa wanda ya yi wa yar wata uku fyade

Hukunci
Daga Justina Auta
Abuja, Yuli 22, 2025 (NAN) Ministar Harkokin Mata da Cigaban Jama’a, Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta yaba da hukuncin daurin shekaru 21 da aka yanke wa Ahmadu Yaro, wanda ya lalata yar wata uku a kauyen Adogi da ke jihar Nasarawa.

A cikin wata sanarwa a ranar Talata a Abuja, ministan ta ce hukuncin da Mai Shari’a Aisha Bashir-Aliyu, Babban Alkalin Nasarawa ta yanke, a matsayin wani mataki mai karfin hali da muhimmi na kare yara masu rauni a cikin al’umma.

ta ce “wannan hukuncin tabbaci ne na rawar da tsarin shari’a ke takawa wajen kare yaranmu.’’

Yayin da ministan take yaba wa jagorancin da Mai Shari’a Bashir-Aliyu ta nuna, ta ce Babban Lauyan jihar, Mista Isaac Danladi, ya jajircecce ne, wanda aka gani a kotu yana nuna muhimmancin hukumomi wajen magance cin zarafi.

Ta kuma nuna godiya ga Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa saboda samar da yanayi mai kyau inda za a iya gudanar da shari’a.

A cewarta, hukuncin yana nuna muhimmin alkawari daga jihar don kare lafiya da mutuncin mata da yara.

Ta kara da cewa “hukuncin ba kawai nasara bane ga iyalin wanda aka zargi amma wata babbar sanarwa ce cewa za a ki yarda da tauye hukunci a jihar Nasarawa.’’

Minista ta jaddada mahimmancin aiwatar da Dokar Hakkin Yara (CRA), wanda aka dora a dukkan jihohi 36.

Ta jaddada hakkin Ma’aikatar kan tabbacin cewa za a kama wadanda suka aikata laifukan yi wa yara fyade, kuma waɗanda suka tsira suna samun kulawa da goyon bayan da ya dace.

Sulaiman-Ibrahim ta ce a ƙarƙashin Tsare-tsaren Shugaban kasa Bola Tinubu, za a daina yin watsi da ko rage hanzarta kan aikata laifuka ga yara da mata.

Saboda haka, sai tayi kira ga sauran jihohi da su bi misalin Nasarawa, tare da bukatar iyalai, al’umma, hukumomin tsaro, da tsarin shari’a su hada kai wajen gina Najeriya mafi lafiya ga duk yara.

Ta ce hukuncin zai zama adalci ga wanda aka zalunta, da gargadi ga wasu.

NAN ta ruwaito cewa lamarin, wanda ya faru a 2020, ya haifar da fushin kasa baki daya, kuma yanzu ya kai ga hukunci bayan shekaru biyar na shari’a.

Mai laifin zai yi zaman kurkuku ba tare da zabin tara ba. (NAN)(www.nannews.ng.com)
JAD/SH
=======
Sadiya Hamza ce ta gyara


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *