Tinubu ya canza sunan UNIMAID zuwa sunan Buhari
Tinubu ya canza sunan UNIMAID zuwa sunan Buhari
UNIMAID
Daga Muhyideen Jimoh
Abuja, 19, ga Yuli, 2025 (NAN) Shugaba Bola Tinubu a ya canza sunan Jami’ar Maiduguri (UNIMAID), Borno, zuwa sunan tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Tinubu ya bayyana wannan yayin taron musamman na Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a Abuja.
Taron an gudanar da shi ne don girmama marigayi shugaba Buhari da ya rasu yana da shekara 82 ranar 13 ga watan Yuli a London bayan rashin lafiya.
A taron wanda ya samu halarchin shugabannin Majalisun Kasa, jami’an gwamnati da iyalan Buhari, Tinubu ya yabawa gado na Buhari na tsari, kaunar kasa, da inganci, yana bayyana rayuwarsa a matsayin wanda yake cike da jaruntaka da hidima wa kasa.
Tinubu yace “yau, muna taro a ƙarƙashin inuwa mai tsanani saboda rashin tshohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
“Muna haduwa ne don girmama wanda ya taba jagorantar wannan dakin, wanda ra’ayinsa ba ya taba fuskantar tangarda, ko da a lokacin da aka zarge shi da ra’ayoyin jama’a masu karfi.”(NAN)(www.nannews.ng)
MUYI/MNA
=========
Maureen Atuonwu ce ta gyara