Tinubu ya bukaci Okpebolo da ya yi amfani da nasarar kotun koli don ci gaba da kyawawan ayyuka
Tinubu ya bukaci Okpebolo da ya yi amfani da nasarar kotun koli don ci gaba da kyawawan ayyuka
Okpebhol
Daga Muhyideen Jimoh
Abuja, Yuli 11, 2025 (NAN) Shugaban kasa Bola Tinubu ya taya Gwamna Monday Okpebholo na Edo murnar nasarar da ya samu a kotun koli, inda ya bukace shi da ya yi amfani da ita wajen kawo ci gaba cikin sauri a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Mista Bayo Onanuga ya fitar ranar Alhamis a Abuja.
Tinubu ya yi maraba da hukuncin da kotun ta yanke a matsayin wani ci gaba ga harkokin mulki, yana mai kira ga gwamnan da ya kasance mai
girmama nasarar tare da hada kan daukacin ‘yan jihar Edo kan manufa daya don samun ci gaba.
Tinub ya ce “Yanzu da gwamnan ya warware matsalolin shari’a, lokaci ya yi da ya kamata ya gaggauta samar da ayyuka na musamman da kuma shugabanci nagari ga al’ummar jihar Edo, wanda tuni ya fara aiwatarwa.”
Ya kuma taya jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta jihar Edo murna, inda ya yi kira da a hada kai da kuma jajircewa wajen gudanar
da aikin da jama’a suka dora masa.
Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa, a wani mataki na bai daya da kwamitin mutane biyar karkashin jagorancin mai shari’a Mohammed Garba, kotun kolin ta yi watsi da zargin rashin cancantar, karar da dan takarar jam’iyyar PDP, Asuerinme Ighodalo,
ya shigar na soke sakamakon zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 21 ga watan Satumba, 2024.
A cewar kotun kolin, ba ta sami dalilin yin watsi da hukunce-hukuncen kotunan daukaka kara da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Edo ba, wadanda suka mayar da Okpebolo na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a matsayin wanda ya lashe zaben
fidda gwani na gwamna.
Ya yi nuni da cewa mai shigar da kara ya kasa gabatar da sahihiyar hujjoji da za su tabbatar da ikirarinsa na cewa zaben ya tafka kura-kurai da suka hada da yawan kuri’u da rashin bin ka’idojin dokar zabe.
Hakazalika, wanda ya shigar da kara ya kasa kiran shaidun da suka dace don nuna wasu shaidun da ya gabatar na goyon bayansa, musamman na Bimodal Voter Accreditation System, BVAS, inji shi.(NAN)(www.nannews.ng)
MUYI/SH
========
Sadiya Hamza ce ta gyara