Bindir ya bukaci masana su mayar da hankali kan bukatun ‘Yan Najeriya

Bindir ya bukaci masana su mayar da hankali kan bukatun ‘Yan Najeriya

Spread the love

Bindir ya bukaci masana su mayar da hankali kan bukatun ‘Yan Najeriya

Sen. Adefemi Kila da sauran masu ruwa da tsaki a taron na farko Engr. Sen. Adefemi Kila taron shekara-shekara colloquium a Abuja.

Bincike

By Angela Atabo

Abuja, Maris 10, 2025 (NAN) An bukaci masu bincike a Najeriya da su mai da hankali kan kirkire-kirkire da kere-kere da za su biya bukatun mutanen kasa.

Dokta Umar Bindir, tsohon Darakta-Janar na Ofishin Samar da Fasaha da Ci Gaban Kasa (NOTAP) ne ya bayar da wannan umarni a wurin taro na shekara-shekara Sen. Adefemi Kila a Abuja.

A jawabin da ya gabatar a wajen taron, Bindir ya ce, abin takaici ne yadda ake gudanar da bincike-bincike a kasa da dama da ba a kebance su ba wajen magance matsalolin cikin gida.

Shi Bindir wanda tsohon sakataren gwamnatin jihar Adamawa ya fusata kan rashin shigar da kimiyya da fasaha cikin tsare-tsare cikin dabarun ci gaban kasa.

Ya ce har yanzu Najeriya ba za ta yi cikakken amfani da gudummawar da al’ummarta na kimiyya ke bayarwa ba, musamman wajen hada ci gaban da aka samu wajen samun mafita.

“Akwai buƙatar samun manufofin masu tushe waɗanda ke yin daidai da abin da ake buƙata, tare da cikakkun bayanai

“Muna buƙatar ɗaukar waɗannan hanyoyin a zahiri kuma mu aiwatar da su azaman sabbin abubuwa, ta yadda za mu iya fara ganin samfuran Najeriya, cikin ƙwarewa,” in ji shi.

Bindir ya ba da shawarar hadin gwiwa mai karfi tsakanin gwamnati, jami’o’i da masana’antu don shawo kan kalubalen.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa taken taron shi ne, “Briding Nigeria’s Infrastructural Gap: Financing, Innovation and Sustainable Policys’’. (Samar da Albarkatun Kasa cikin ci gaba da kwarewa)

Ya umurci masu bincike na Najeriya, masu kirkiro da su mayar da hankali kan ayyukansu wajen magance matsalar karancin ababen more rayuwa kamar, rashin isassun hanyoyi, hanyoyin jiragen kasa, karancin wutar lantarki, da rashin ingantaccen ruwan sha wanda aka dade tsawon shekaru.

NAN ta ruwaito cewa taron ya samu halartar tsohon shugaban kasa, Gen.Yakubu Gowon, tsohon ministan yada labarai, Farfesa Jerry Gana wanda, ya yaba da gudunmawar da Kila ya bayar a fannin injiniya.

Shugabar kungiyar Injiniyoyi (NSE), Margaret Oguntala wanda Ali Rabiu ya wakilta, tsohuwar mataimakiyar shugaban NSE ta bayyana Kila a matsayin tambarin injiniya ta kara da cewa gudummawar da ya bayar ta taimaka wajen samar da wannan sana’a.

Shugaban Cibiyar Injiniyoyi ta Najeriya (NICE), Tokunbo Ajanaku, ya ce Kila ya yi aikin injiniya sama da shekaru 50 yana horar da matasa da dama tare da taimakawa wajen sauya yanayin aikin injiniya a Najeriya.

“Muna fatan aiwatar da duk kyawawan abubuwan da muka koya a wannan taron, muna fatan Najeriya za ta inganta ta dalilin wannan taron,” in ji shi.

A martanin da ya mayar, mai bikin ya godewa ‘yan uwa da abokan arziki da abokan aikin sa bisa shirya taron don karrama shi. (NAN) ( www.nannewse.ng )

ATAB/ROT

========

Rotimi Ijikanmi ne ya gyara shi


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *