Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin mutane 6 kan rikicin neman sauyin tsarin mulki
Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin mutane 6 kan rikicin neman sauyin tsarin mulki
Kwamitin
Muhammad Nur Tijjani
Kano, Maris 5, 2025 (NAN) Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamiti mai mutum shida domin aiwatar da shawarar kwamitin bincike kan rashin zaman lafiya a lokacin neman sauyin tsarin mulki ya jawo.
Da yake kaddamar da kwamitin a ranar Talata a Kano, Gwamna Abba Yusuf, ya ce kwamitin an rataya masa yin nazari sosai kan rahoton tare da ba da shawarwarin da za su hana faruwar abun a nan gaba.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Umar Ibrahim, ya bayyana abubuwan da suka faru a matsayin wani abu mai raɗaɗi.
A cewarsa, hasarar rayuka da barnata dukiyoyin da aka kiyasta sun kai biliyoyin nairori sun kawo koma baya ga jihar.
Gwamnan ya jaddada aniyar gwamnati na daukar duk matakan da suka dace domin hana sake afkuwar lamarin, da sake gina tattalin arziki, da kuma rage radadin da rikicin ya haifar.
Gwamnan yayin da yake bayyana muhimmiyar rawar da kwamitin ke takawa, ya bayyana kwarin gwiwar cewa kwarewar mambobinsa za ta tabbatar da daukar matakin da ya dace a kan lokaci kuma mai inganci.
Kwamitin yana karkashin jagorancin Alhaji Dan Yahaya, babban sakataren ma’aikatar tsaro da ayyuka na musamman; Alhaji Aliyu Garo, babban sakataren ma’aikatar matasa da wasanni, memba; da Dr Hadi Bala, babban sakataren ma’aikatar ilimi mai zurfi, memba.
Sauran su ne Salisu Marmara – ma’aikacin ma’aikatar shari’a; Malam Yahaya Umar, Daraktan tsare-tsare, bincike da kididdiga, amintaccen asusun fansho na jihar Kano, sakatare; da Jamilu Usman, Mataimakin Sakatare II, REPA Directorate, ofishin SSG, don zama Mataimakin Sakatare.
Da yake jawabi a madadin ‘yan kwamitin, Yahaya ya bayyana godiyarsa ga gwamnatin jihar Kano da Gwamna Yusuf bisa wannan muhimmin aiki da suka ba su.
Ya kuma ba da tabbacin gwamnati cewa kwamitin zai yi aiki tukuru domin tabbatar da amincewar da aka yi musu.(NAN) www.nannews.ng
MNT/MAM/SH
=========
Edited by Modupe Adeloye/Sadiya Hamza