PDP ta bukaci musulmi da su yi amfani da watan Ramadan wajen inganta hadin kan kasa
PDP ta bukaci musulmi da su yi amfani da watan Ramadan wajen inganta hadin kan kasa
Azumi
Daga Habibu Harisu
Sokoto, Maris 3, 2025 (NAN) Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Amb. Umar Damagum, ya yi kira ga musulmi da su yi amfani da lokacin azumi Ramadan don inganta hadin kan kasa a tsakanin ‘yan Najeriya.
Damagun ya yi wannan kiran ne a cikin sakonsa na watan Ramadan na shekarar 2025 da ya mika wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Lahadi a Sokoto.
A cikin wata sanarwa ta hanyar
Babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa, Malam Yusuf Dingyadi, Damagun, ya bukaci musulmi da su sadaukar da kansu wajen addu’o’in neman zaman lafiya, ci gaba da ci gaban Nijeriya.
Ya jaddada cewa Najeriya na bukatar kwanciyar hankali da hadin kai a siyasance, musamman ganin irin kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta a halin yanzu, yana mai cewa, “wannan ya zama abin damuwa ga ci gabanmu a matsayinmu na kasa baki daya.”
Damagun ya bukaci masu hannu da shuni da su mika hannun zumunta da kauna fiye da iyalansu domin baiwa sauran marasa galihu damar amfana.
Daga nan sai ya hori musulmi da su yi koyi da salon rayuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, wanda ya jaddada muhimmancin karamci, musamman a cikin watan Ramadan. (NAN) (www.nannews.ng)
HMH/KLM
========
Muhammad Lawal ne ya gyara