Gwamna Makinde yayi alhinin mutuwar Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin
Gwamna Makinde yayi alhinin mutuwar Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin
Makoki
By David Adeoye
Ibadan, Maris 3, 2025 (NAN) Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ya bayyana marigayi Sarkin Sasa na Ibadan, Alhaji Haruna Maiyasin a matsayin jajirtaccen jagora kuma mai kishin Najeriya ta kowace fuska.
Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi ta bakin babban sakataren yada labaran sa, Dr Sulaimon Olanrewaju, a Ibadan.
Da yake jajanta wa kan rashin Sarkin Sasa, wanda ya rasu a yammacin ranar Asabar, gwamnan ya ce rasuwarsa ta kawo karshen babban zamani.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa Marigayi Maiyasin shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Arewa a Jihohin Kudancin Najeriya 17.
Makinde ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan Alhaji Maiyasin da daukacin al’ummar Hausa/Fulani na Jihar Oyo da Kudancin Najeriya.
Ya yi addu’ar Allah ya jikan marigayin.
A cikin sanarwar, gwamnan ya bayyana cewa dangantakarsa da marigayi Maiyasin ta dade da dadewa, tun kafin ya zama gwamnan jihar.
“Rasuwar Alhaji Maiyasin yana da shekaru 125 ya kawo karshen babban zamani.
“Ya kasance babban shugaba wanda ya jagoranci jama’arsa da jajircewa tare da nuna kishin kasa ga jihar Oyo da Najeriya ta kowace fuska.
“Hadin gwiwarsa da gwamnatinmu abin koyi ne,” in ji Makinde.(NAN)(www.nannews.ng)
DAK/AMM
======
Abiemwense Moru ne ya gyara