‘Yan sanda sun kama mutum 6 da laifin yin barna, da karbar kayan sata a Jigawa
‘Yan sanda sun kama mutum 6 da laifin yin barna, da karbar kayan sata a Jigawa
Kama
Daga Muhammad Nasir Bashir
Dutse, Maris 3, 2025 (NAN)Rundunar ‘yan sanda a jihar Jigawa, ta kama wasu mutane shida da ake zargi da aikata barna a karamar hukumar Kazaure ta jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Lawan Shiisu, ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar a Dutse ranar Litinin.
Shiisu ya ce, biyar daga cikin wadanda ake zargin, masu shekaru tsakanin 28 zuwa 53, an kama su ne da laifin yin barna, yayin da wanda ake zargi na shida mai shekaru 30 da haihuwa, an kama shi bisa zargin karbar kayayyakin sata.
Ya bayyana cewa, an kama biyu daga cikin wadanda ake zargin ne a ranar 26 ga watan Fabrairu bayan da ake zarginsu da lalata fitulun titi, wayoyi masu sulke da kuma wayoyi masu amfani da magudanar ruwa a yankin Bandutsi na karamar hukumar.
Ya kara da cewa an kama wasu mutane uku da ake zargi a ranar 28 ga watan Fabrairu bayan da ake zarginsu da hada baki wajen lalata wayar tarho mai tsawon mita 2,000 a kauyukan Faru da Daba na karamar hukumar.
A cewarsa, a yayin da ake yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun bayyana Musa Yahaya dan shekara 30 daga yankin Wajen Gabas da ke cikin garin Kazaure a matsayin abokinsa kuma mai karbar kayan da suka sace.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya yi zargin cewa Yahaya na sane da cewa wayoyin na gwamnati ne kuma an sace su.
Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa, tuni aka gurfanar da su gaban kotu.(NAN) (www.nannews.ng)
MNB/KO
=========
Kevin Okunzuwa ne ya gyara

