Ramadan: Sarkin Daura ya bukaci a tallafa wa mabukata
Ramadan: Sarkin Daura ya bukaci a tallafa wa mabukata
Daga Aminu Daura
Ramadan
Daura (Jihar Katsina), Maris 1, 2025 (NAN) Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk, ya bukaci al’ummar Musulmi da su rika kai agaji ga marasa galihu a duk tsawon wannan wata na Ramadan.
Sarkin ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Asabar a fadarsa da ke Daura.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci na Ramadan wajen neman kusanci zuwa ga Allah ta hanyar gudanar da ayyukan alheri da addu’o’in neman gafara da addu’o’in zaman lafiya da ci gaban jihar da kasa baki daya.
“Azumi yana karfafa tarbiyyar kai kuma yana tunatar da musulmi da su yi aiki da abin da zai faranta wa Allah rai. Wannan tunani yana taimaka wa mabiya su ƙarfafa dangantakarsu da Mahaliccinsu.
“Ina kira ga mutane mawadata da su taimaka wa marasa galihu da matalauta da abinci da sauran kayayyaki a cikin Ramadan,” in ji Sarkin.
Ya kuma taya al’ummar musulmi murnar ganin wata mai alfarma na Ramadan, inda ya kara da cewa kamata ya yi a yi amfani da irin wannan gata wajen samar da zaman lafiya a tsakanin kungiyoyin addinai a jihar da ma Najeriya baki daya.
A wani labarin kuma, Shugaban karamar hukumar Daura, Alhaji Bala Musa, ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su kara kyautata makwabtaka da kyautatawa mabukata a cikin watan Ramadan.
Ya ce ya kamata lokacin azumi ya zama lokacin tunani da addu’a da kuma kula da juna. (NAN) www.nannews.ng
AAD/ YMU
Edited by Yakubu Uba