Ramadan: Fintiri ya bukaci musulmai su yi addu’a don zaman lafiya, hadin kai

Ramadan: Fintiri ya bukaci musulmai su yi addu’a don zaman lafiya, hadin kai

Spread the love

Ramadan: Fintiri ya bukaci musulmai su yi addu’a don zaman lafiya, hadin kai

Addu’a

Daga Ibrahim Kado

Yola, Maris 1, 2025 (NAN) Gwamna Ahmadu Fintiri na Jihar Adamawa ya bukaci al’ummar Musulmi da su yi amfani da lokacin watan Ramadan wajen addu’ar zaman lafiya da hadin kan kasa baki daya.

Fintiri ya yi wannan kiran ne a wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Mista Humwashi Wonosikou ya fitar ranar Asabar a Yola.

Gwamnan ya kuma bukaci mabiya addinai daban-daban da su so juna su zauna lafiya, wanda ya ce an san jihar da halayyar.

“Ina taya al’ummar Musulmi a jihar da ma duniya baki daya murnar ganin watan Azumin Ramadan, saboda dama ce a shaida cikin shekarar 2025.

“Ina kira gare ku da ku yi amfani da wannan lokaci wajen neman kusanci zuwa ga Allah da kuma sadaukar da kanku ga koyarwar Alkur’ani mai girma kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya koyar.

“Yayin da muke neman yardar Allah a cikin wannan wata mai alfarma, mu rike wadannan darussa na Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam tare da yin addu’o’in neman zaman lafiya a kasar nan.

“A matsayinmu na mutane, za mu iya cimma abubuwa da yawa a cikin yanayi na lumana, abin da ake bukata shi ne soyayyar juna da jajircewa wajen yin aiki da zaman lafiya da hadin kan kasarmu,” in ji shi.

A cewarsa, watan Ramadan ya sake ba wa musulmi damar sake sadaukar da kansu ga bautar Allah.

Fintiri ya bukaci musulmin muminai da su kasance masu lura a wuraren ibada.
“Mun sanya dukkan gine-gine don tabbatar da tsaron mazauna, amma har yanzu dole ne ku yi taka tsantsan.”

Gwamnan wanda ya yi nuni da cewa al’ummar kasar na cikin bakin ciki da ganin yadda ake samun karuwar rarrabuwar kawuna da tabarbarewar tsaro a ‘yan kwanakin nan, ya bukaci ‘yan Nijeriya da su hada kai domin ganin an kawo karshen wannan lamari (NAN) (www.nannews.ng)
IMK/EOB/YMU
==========
Edith Bolokor da Yakubu Uba ne suka shirya.

 


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *