Gwamnatin Sokoto za ta kashe miliyan 998 akan shirin ciyarwa na watan Ramadan

Gwamnatin Sokoto za ta kashe miliyan 998 akan shirin ciyarwa na watan Ramadan

Spread the love

Gwamnatin Sokoto za ta kashe miliyan 998 akan shirin ciyarwa na watan Ramadan

Ciyarwa

Daga Habibu Harisu

Sokoto, Feb. 25, 2025 (NAN) Gwamnatin jihar Sokoto ta ware naira miliyan 998 don shirin ciyarwa na watan Ramadan na shekarar 2025.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa shirin ciyarwar zai gudana ne a cibiyoyin ciyar da abinci guda 155 da aka kebe a fadin jihar.

Da yake jawabi a wajen rabon kayan abinci ga manajojin cibiyoyin ciyarwa a ranar Talata a Sokoto, Gwamna Ahmad Aliyu ya ce kowace cibiya za ta samar da kayan abinci iri-iri da na dafa abinci.

A cewarsa, mutane 1,400 ne aka dau nauyin yin su hidima ciki har da mata 610 a matsayin masu dafa abinci.

Ya ce sama da mutane 20,000 ne ake sa ran ciyar da su a kowace cibiya a kullum har zuwa karshen azumin Ramadan.

Aliyu, wanda ya baiwa manajojin cibiyoyin shawara kan yin gaskiya, ya kuma bukaci mazauna yankin da su tabbatar da zaman lafiya a yayin aikin.

Gwamnan ya bayyana cewa an kuma raba buhunan masara guda 990 ga malaman addini 2,400 a wani bangare na shirin tallafin azumin watan Ramadan.

Ya ce kowane limamin masallaci ya karbi buhunan masara guda biyar da naira 100,000, mataimakan limaman kuma sun samu buhunan masara guda uku da naira 50,000 kowanne, yayin da aka ba wa Masu kiran salla buhunan masara guda biyu da naira 50,000 kowanne.

Aliyu ya kara da cewa, an kuma baiwa malaman addinin musulunci guda 300 da aka zabo daga unguwanni Naira 200,000 kowannensu, yayin da wasu malamai 100 kuma aka baiwa kowannensu Naira 100,000.

Gwamnan ya ci gaba da cewa an zabo malaman kur’ani guda 10 (Malaman Zaure) daga kowace shiyya ta kananan hukumomi 23 domin karbar Naira 50,000 kowacce.

Ya ce sun yi hakan ne da nufin karfafa musu gwiwa ta yadda za su ci gaba da gudanar da ayyukan addini tun daga tushe.

“Wannan tallafin an yi shi ne domin a taimaka musu da iyalansu, da nufin ba su damar mai da hankali kan muhimman ayyukan da suka rataya a wuyansu na addini a cikin wannan lokaci mai alfarma.

“Wannan al’amari na nuna godiya ga dimbin gudunmawar da malamai ke bayarwa ga al’ummar jihar domin ganin an tafiyar da harkokin addinin musulunci musamman a matakin farko ba tare da cikas ba,” in ji Aliyu.

A nasa jawabin kwamishinan harkokin addini Dr Jabir Maihula ya ce an fadada atisayen ne tun a shekarun baya, inda ya ce an fara gudanar da atisayen ne a zamanin gwamnatin tsohon Gwamna Aliyu Wammako.

Maihula ya ce shirin ciyar da watan Ramadan ya samar da ayyukan yi ga mutane da dama tare da inganta harkokin kasuwanci a jihar. (NAN)(www.nannews.ng)
HMH/YMU
Edited by Yakubu Uba
=====

 

 

 

 


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *