NAFDAC ta gargadi matasa kada ku bari shaye-shayen muggan kwayoyi su lalata rayuwar su
NAFDAC ta gargadi matasa kada ku bari shaye-shayen muggan kwayoyi su lalata rayuwar su
Shaye-shaye
Daga Rita Iliya
Minna, Fabrairu 5, 2025 (NAN) Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta gargadi ‘yan
Najeriya, musamman matasa kan shaye-shayen miyagun kwayoyi, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana ga makomar kasar.
Farfesa Christianah Adeyeye, Shugabar ta NAFDAC ce ta bayyana haka a ranar Laraba a yayin wani taron wayar da kan jama’a mai taken “Catch Them Young”
da aka gudanar a makarantar sakandiren Muhammadu Kobo da ke karamar hukumar Lapai a jehar Neja.
Adeyeye, wanda Jami’in jihar, James Kigbu, ya wakilta, ya ce an tabbatar da cewa ‘yan Najeriya miliyan sha hudu da dubu ɗari uku ne suka kamu da shan miyagun kwayoyi.
A cewar Adeyeye, kididdigar na da matukar tayar da hankali, don haka akwai bukatar hada karfi da karfe domin yakar wannan barazana.
Ta ce shirin “Catch Them Young”, an tsara shi ne domin rage yawaitar shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin daliban makarantun sakandare.
Shugabar NAFDAC din ta nuna damuwa game da haramtattun abubuwa da ke iya samuwa da cikin sauki, kamar barasa da taba.
Tace “lokacin samartaka lokacin gwajine, wanda shine inda matsalar ke farawa.
“Ya kamata dalibai su dauki yaki da shan miyagun kwayoyi da muhimmanci domin yaki ne don makomar Najeriya.”
Shugaban makarantar, Dr Abubakar Mohammed, ya yabawa hukumar NAFDAC bisa sake kafa kungiyar tare da shawartar daliban da su guji shan miyagun kwayoyi.
Har ila yau, Mista Abdulmalik Ndagi, shugaban kungiyar shugabannin makarantun sakandire ta Najeriya (ANCOPSS) na jihar, ya bayyana farin cikinsa da yadda NAFDAC ke nuna damuwa ga makomar matasa.
Ya bukaci hukumar da ta ci gaba da kokarinta na yakar shaye-shayen miyagun kwayoyi.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa an sake kafa kungiyar kare hakkin masu amfani da kayayyaki ta NAFDAC (NCSC) a makarantar, inda dalibai 175 suka bude a matsayin mambobi. (NAN)(www.nannews.ng)
RIS/AYO/
=======
Ayodeji Alabi da Hadiza Mohammed-Aliyu suka gyara