Jihar Jigawa ta amince da Naira 4.8 don ciyarwar azumi

Jihar Jigawa ta amince da Naira 4.8 don ciyarwar azumi

Spread the love

Jihar Jigawa ta amince da Naira 4.8 don ciyarwar azumi

Azumi
By Aisha Ahmed

Dutse, Janairu 28, 2025 (NAN) Gwamnatin jihar Jigawa, ta amince da kashe Naira biliyan hudu da dubu dari takwas don ciyar da mutane a watan azumin Ramadana na shekarar 2025 a fadin kananan hukumomi 27 na jihar.

Mista Sagir Musa, kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Dutse, yayin da yake zantawa da manema labarai sakamakon taron majalisar zartarwa.

Musa ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta amince da karin cibiyoyin ciyar da watan Ramadana daga 609 zuwa 630.

A cewarsa, daukacin shirin ciyarwar a watan Ramadana, gwamnatin jihar da kuma kananan hukumomi za su dauki nauyin gudanar da ayyukan.

“Gwamnatin jihar za ta bayar da kashi 55 cikin 100 yayin da kananan hukumomi ke da kashi 45 cikin 100.

“Kowace unguwanni 287 da ke jihar za ta samu mafi karancin cibiyoyin ciyar da abinci guda biyu baya ga Masallatan Juma’a, gidajen yari, wuraren gyara motoci, wuraren ajiye motoci da kasuwanni, da kuma manyan makarantun jihar 15.”

Kwamishinan ya kara da cewa gwamnatin jihar ta kuma kafa kwamitin aiwatar da shirin ciyar da abinci.(NAN)(www.nannews.ng)

AAA/DCO

========


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *