Zaben shugabanni PDP a Kaduna ya bar baya da kura
Zaben shugabanni PDP a Kaduna ya bar baya da kura
Daga
Ibrahim Bashir
Kaduna, Sept. 25, 2024 (NAN) Alamu na nuni da cewar zaben shugabannin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Kaduna ya bar baya da kura domin, Danjuma Sarki, daya daga cikin masu takara ya nuna rashin amincewa.
Sarki ya bayyana hakane a lokacin da ya ya yi magana da ‘yan jaridu ranar Laraba kaduna.
Dantakarar yayi korafin rashin amincewa da zaben wanda a cewarsa ba’ayi zabe nagariba domin wadanda suka shirya zaben sun yi amfani da kuri’un da ba tantance su ba.
Ya zargi cewar wasu masu zaben kuma bama ‘ yan jam’iyya bane kuma mafi yawancin kuri’un an shigo dasune ta barauniyar hanyar.
Ya kuma koka da cewar ankori mafi yawancin magoya bayansa tare da tsoratar da wasu.
Sarki ya yi kira ga magabatan jam’iyyar da masu ruwa da tsaki na jama’iyyar da su shigo cikin lamarin don kawo cikakken gyara.
Kamfanin Dillancin Labarun Najeriya (NAN) ya ruwaito cewar amma duk da wannan korafi nasa tuni an rantsar da sababbin jagororin na jam’iyyar kuma an bayyana Mr. Edward Masha, shine wanda aka bayyana yalashe kujerar jagorancin jam’iyyar,
Masha, yagode wa dukkanin magoya bayansa sannan yaja hankalin wadanda suka fadi da su rungumi kaddara su zo agina Sabuwar jam’iyya don cigaban al’umma baki daya.
Ya amshi Shugabacin jam’iyyar daga Hassan Hyab, wanda wa’adinsa ya kare. (NAN)
IB