Tinubu ya nuna jimamin mutuwar Mai Shari’a Ayoola

Tinubu ya nuna jimamin mutuwar Mai Shari’a Ayoola

Spread the love

Tinubu ya nuna jimamin mutuwar Mai Shari’a Ayoola

Jimami

By Salif Atojoko

Abuja, Aug. 22,2024 (NAN) Shugaban Kasa Bola Tinubu ya yi ta’aziya ga iyalan Marigayi Mai Shari’a Emmanuel Ayoola.

Sakon ta’aziyar na kunshe ne a wani bayani da Mai bada Shawara ga shugaban kasar kan harkokin yada labarai, Chief Ajuri Ngelale ya bayar a yau Alhamis a Abuja..

A ta bakin Ngelale, Tinubu ya yaba da kokari, halin dattako da juriya na marigayin.

Tinubu ya kara da cewa za’a ci gaba ba tunawa da Ayoola saboda halayen sa na hakuri, fasaha, da’a da dumbin kwarewa na Shari’a.

Shugaban kasar yayi addu’ar samun rahama ga marigayin haka Kuma Allah ya ba iyalan sa hakurin jure wannan babban rashin.

Kamfanin dillacin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Marigayi Ayoola Alkalin Kotun Koli ne Mai ritaya.

Ya kuma taba zama Shugaban Ma’aikata Mai yaki da cin hanci, rashawa da sauran laifuka watau, ICPC.

Marigayi Ayoola kwarraren Lauya ne Kuma tsohon jami’in shari’a wanda ya taba Alkali Kotun Daukaka Kara ta Kasar Gambiya daga shekarar 1980 zuwa 1983.

Ya kuma zama babban Mai Shari’a na Kasar Gambiyan daga shekarar 1983 zuwa 1992.

Marigayi Ayoola ya kuma taba zama Shugaban Kotun Daukaka Kara na Kasar Seychelles da kuma zama Mai Shari’a a Kotun Daukaka Kara ta Najeriya daga shekarar 1992 zuwa 1998. (NAN) (www.nanmnews.ng)

SA/VIV/BRM
===============
Edited by Vivian Ihechu/ Tacewa: Bashir Rabe Mani


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *