Najeriya za ta iya cin gajiyar dala Amruka biliyan 100 a kasuwannin magani a duniya – cewar Masaniya
Najeriya za ta iya cin gajiyar dala Amruka biliyan 100 a kasuwannin magani a duniya – cewar Masaniya
Magani
Daga Alaba Olusola Oke
Ondo (Jihar Ondo), 30 ga Agusta, 2024 (NAN) Wata Ma’aikaciyar harhada magunguna, Misis Zainab Shariff, ta ce Najeriya za ta iya cin gajiyar dalar Amruka biliyan 100 a kasuwannin magani ta duniya.
Ta bayyana hakan ne a yayin bikin ranar maganin gargajiya na Afirka, wanda Cibiyar Nazarin Magungunan Gargajiya da Bincike ta Jami’ar Kimiyyar Lafiya (UNIMED) Ondo ta shirya a ranar Alhamis.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa taron mai suna “Hadawa da Inganta Magungunan Gargajiya na asali don Saukake Kiwon Lafiyar ” wanda a ka shirya a garin Ondo.
Shariff, wadda wata kwararriyar mai fafutuka ce na inganta Magungunan Gargajiya da na Asali (TCAM) Najeriya ce ta bayyana haka.
Masaniyar ta ce yin amfani da kasuwannin duniya don samar da irin magungunan zai samar da kusan dala tiriliyan biyar nan da shekarar 2050 a duniya.
A cikin makalarta ta mai taken “Haɓaka da Ci gaban Tsirrai na Magani don Samar da Kiwon Lafiya a Duniya” ta jaddada buƙatar ƙara darajar magungunan da ake da su a ƙasar nan don fitar da su zuwa kasashen waje.
Gaskiyar halin da ake ciki yanzu, a cewarta, ba a nuna kasar Najeriya wajen fitar da tsire-tsire masu magani zuwa kasashen waje ba, duk da dimbin albarkatun da take da su.
Sai dai ta kara da cewa har yanzu akwai fata ga kasar idan har al’ummar kasar za su iya tantance filayen noman tsire-tsire na magani don kara darajarsu.
Masaniyar harhada magungunan ta ce kasar za ta iya samar da magungunan ganye da ire-iren su da za su shiga jerin amicewar hukumar ta NAFDAC zuwa kantuna daban-daban don tallafawa ci gaba da bincike.
Ta ba da shawarar cewa ya kamata kasar ta fadada hadin gwiwarta da masu ruwa da tsaki tare da aiwatar da shirye-shiryen digiri a fannin likitancin tsire-tsire.
A nasa jawabin, mataimakin shugaban Jami’ar UNIMED ta Ondo, Farfesa Adesegun Fatusi, ya ce tuni cibiyar ta dauki nauyin gudanar da karatun digiri na uku a fannin likitancin tsire-tsire.
Ya ce “a wani bangare na habakar huldar, cibiyar ta bayyana fa’idar magungunan ganye da tsire-tsire, ta kuma kafa Sashen fannin Magungunan da za su fara digiri na farko a shirin a watan Oktoba 2024.”
A nasa bangaren, Dokta Oghale Ovuakporie-Uvo, Darektan riko na cibiyar kula da magungunan tsire-tsire da ganye tare da gano magunguna, ya nanata kudurin cibiyar na gano magungunan ganye da tsire tsire domin saukaka harkokin kiwon lafiya a duniya.
Ovuakporie-Uvo ya ce fahimtar shirin shine tushe da kuma amfani da hankali na magungunan gargajiya na asali, musamman al’adun gargajiya da na lafiya dangane da amfani da tsire-tsire da ganye wanda ke da mahimmanci samar da cikakkiyar lafiya a yanayin mutanen Afirka. (NAN) (www.nannews.ng)
OKEO/HA
=======
Hadiza Mohammed-Aliyu ta gyara