NAN HAUSA

Loading

Matawalle ya bukaci shugaban hafsoshin Najeriya ya gaggauta kamo ma kisan Sarkin Gobir 

Matawalle ya bukaci shugaban hafsoshin Najeriya ya gaggauta kamo ma kisan Sarkin Gobir 

Spread the love

Matawalle ya bukaci shugaban hafsoshin Najeriya ya gaggauta kamo ma kisan Sarkin Gobir

 

 

Kisa

Daga Deborah Coker

Abuja, Aug. 23, 2024 (NAN) Dakta Bello Matawalle, Karamin Ministan Tsaron Najeriya, ya bukaci shugaban rundunar hafsoshin sojojin Najeriya, Janar Christopher Musa, da ya gaggauta kamo waɗanda suka kashe Sarkin Gobir na Gatawa a Jahar Sakkwato, Alhaji Isa Bawa.

 

Matawalle ya bada umarnin ne a wata sanarwa da jami’in yada labarai da ke Ma’aikatar Tsaron Najeriya, kuma  Mista Henshaw Ogubike, ya fitar a ranar Juma’a a Abuja.

 

A cewar sa, ministan wanda yayi Allah wadai da kisan gillar da yan bindigar suka yiwa sarkin Gobir din ya jadadda cewa gwamnati ba zata taba aminta da wannan ta’addanci ba.

 

“Kisan Bawa rashin tunanin ne, kuma ta’addanci ne da ba za’a amunce da shi ba. Zamuyi bakin kokarin mu da tabbatar da hukunta waɗanda suka aikata laifin.

 

“A dalilin hakan ne ya zama dole shugaban hafsoshin sojojin Najeriya ya gaggauta kaddamar da nadin masu binciken wannan aika aikar a kuma tabbatar da cewa an gurfanar da su a gaban kotu.

 

“Tsaro na gaba gaba cikin kudirin gwamnatin shugaban Najeriya, Bola Tinubu, wanda kuma ya bai wa rundunar sojojin Najeriya cikakken gooan baya,” a cewar ministan.

 

Matawalle ya kuma tabbatar wa da al’ummar Najeriya cewa babu shakka Rundunar Sojojin Kasar Najeriya ba zasu bar baya da kura ba wajen zakulo waɗanda suka aikata wannan mummunar ta’addancin dan ganin an hukunta su a bisa tsarin dokokin kasa.

 

“Zamu ci gaba da aiki batare da gajiya ba dan tabbatar da tsaro da kwanciyar hankalin al’ummar Najeriya,” a cewar jawabin ministan.

 

Matawalle ya kuma mika ta’aziyarsa zuwa ga iyalan marigayi me martaba Sarkin Gobir tare da dukan al’ummar Gatawa, da na jahar Sakkwato baki daya da kuma gwamnatin jahar.

 

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya yayi rahoton cewa an sace Sarkin ne da daya daga cikin ya’yan sa a lokacin da suke kan hanyar su ta kowowa gida daga Sakkwato yau kwana 26 dai dai tsakanin sace she da kisan gillar da waɗanda suka sace shi suka yi masa.

(NAN)(www.nannews.ng)

 

DCO/SH

========

 

edita by Sadiya Hamza

 

Fassara daga Abdullahi Mohammed/Bashir Rabe Mani

 


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *