Kungiyar Gwamnoni, majalisa ta nemi samawa sarakuna aiki a tsarin mulkin kasa
Kungiyar Gwamnoni, majalisa ta nemi samawa sarakuna aiki a tsarin mulkin kasa
Ayyuka
Daga Salisu Sani-Idris
Abuja, Oktoba 31, 2024 (NAN) Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) da majalisar sarakuna ta kasa sun yi kira da a samar da doka cikin tsarin mulki don samawa sarakuna ayyuka a fadin kasa.
Gwamna Dapo Abiodun na Ogun, ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron hadin gwiwa tsakanin kungiyar NGF da majalisar da aka gudanar a dakin taro na Banquet da ke fadar shugaban kasa a Villa a Abuja.
“Wannan taron irin sa na farko ya kasance ne a taron kungiyar gwamnonin Najeriya, karkashin jagorancin shugaban mu Gwamna AbdulRahman AbdulRazak na jihar Kwara.
“Ajandar ranar, da sauransu, ita ce batun rawar da tsarin mulki zai taka ga sarakunan gargajiya,” in ji shi.
Gwamnan ya ce a halin yanzu akwai kudirin doka a gaban Majalisar Dokoki ta kasa, inda ake neman a ba sarakunan gargajiya rawar da tsarin mulki ya tanada.
“Bayan mun samu ‘yan bayanai daga sarakunanmu, kungiyar Etsu Nupe ta yi mana bayanin yadda kudirin dokar ya kasance, kuma mun amince da kudirin da aka gabatar, kamar yadda aka gabatar,” in ji Abiodun.
Ya ce taron ya kuma amince da a kafa kwamitin hadin gwiwa na gwamnoni da sarakunan gargajiya domin tabbatar da cewa an shigar da maganganun da aka yi a taron a cikin kudirin samar da kwakkwarar takarda.
Ya ce, kudirin na karshe zai kasance wata takarda ce da za ta hada karfi da karfe da za ta kara karfafa gwiwar sarakunan gargajiya, tare da sanya su cikin harkokin mulki, zaman lafiya, tsaro a fadin kasar nan.
Abiodun ya kuma ce taron ya tattauna ne kan zaman lafiya da tsaro, samar da abinci, da duk wata barazana da ta kunno kai.
“Haka zalika an kara jaddada irin rawar da sarakunan mu suka yi, tunda su ne suka fi kusa da talakawa.
“Kuma an yi sa’a, an albarkace mu da da yawa daga cikinsu waɗanda suke da gogewa, masu ilimi; muna da sojoji da suka yi ritaya wadanda ba za a iya kima da gudunmawarsu ba.
“Mun kuma tattauna batutuwan da suka shafi ‘yan sandan jihohi da cin zarafin mata. Mun yi magana game da tasiri, ko akasin haka, cin gashin kan kananan hukumomi ga sarakunan gargajiya.
“Manufar ita ce sanar da su abin da hukuncin Kotun Koli yake nufi, domin su sami kyakkyawar fahimtar tasirin wannan hukuncin idan aka fara aiwatarwa,” in ji shi.
A nasa bangaren, Alhaji Yahaya Abubakar, Etsu Nupe, ya yabawa kungiyar NGF bisa goyon bayan rawar da tsarin mulki ya baiwa sarakunan gargajiya.
Ya tabbatar da cewa taron ya tattauna ne kan yadda za a warware matsaloli, musamman rawar da tsarin mulki ya baiwa sarakunan gargajiya.
“Na gabatar da takaitaccen bayani kan kudirin da ake aikewa Majalisar Dokoki ta kasa, domin kamar yadda kuka sani, a halin yanzu akwai kwamitin da ke da alhakin duba kundin tsarin mulkin kasar na 1999.
“Don haka, mun riga mun gabatar da wani kudiri ga kwamitin da nufin gyara kundin tsarin mulki yadda ya kamata ta hanyar tantance wuraren da muka ambata,” in ji shi.
Ya bayyana cewa tsarin, aiki da kuma kudade na cibiyoyin gargajiya an bayyana su a cikin kudirin dokar.
“Babu wani abu da zai iya faruwa ba tare da ingantaccen kudade ba. Don haka, mun yi imani da ƙarfi cewa idan hukumomin suna samun kuɗi sosai, za mu yi aiki sosai.
Etsu Nupe ya ce “A yanzu cibiyarmu tana da ƙwararru, tare da jami’an soja da suka yi ritaya, masu fasaha da kowane fanni da za ku iya tunani akai,” in ji Etsu Nupe.
Ya bayyana cewa tuni aka kafa wani kwamiti wanda ya kunshi mambobi 15 a karkashin jagorancin Gwamna Hope Uzodima na Imo.
“Kwamitin zai magance wadannan batutuwa sannan ya dawo da rahoto a zauren taron domin a dauki matakan da suka dace,” in ji shi. (NAN) (www.nannews.ng)
SSI/SA
Salif Atojoko ne ya gyara
=============