NAN HAUSA

Loading

Hamada na tilastawa mutane tserewa daga gidajensu a Jihar Yobe – Shugaban hukuma

Hamada na tilastawa mutane tserewa daga gidajensu a Jihar Yobe – Shugaban hukuma

Spread the love

Tapkin Tulo Tulo dake karamar hukumar Yusufari a jihar Yobe

 

Hamada na tilastawa mutane tserewa daga gidajensu a Jihar Yobe – Shugaban hukuma

Hamada
By Nabilu Balarabe
Damaturu, Augusta 30, 2024 (NAN) Kwararowar Hamada na cigaba da tilastawa al’umomi da dama a karamar hukumar Yusufari ta jihar Yobe barin yankunansu na asali.

Shugaban karamar hukumar, Alhaji Baba Aji, ya bayyana hakan ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Damaturu ranar Juma’a.

Ya ce dunkulewar yashi ya mamaye filaye da gidaje a cikin gundumominsu, lamarin da ya hana mutane da dabbobi da yawa cigaba da zama a yankunan.

“ Hamada ta kori mutane da yawa daga asalinsu. Wasu daga cikin wadannan mutanen yanzu haka suna samun mafaka a kauyen daban daban.

“Idan ka je kauyukan da abin ya shafa za ka ga dunkulewar yashi na ci gaba da matsowa kusa da gidaje.

“Wannan lamarin ya tilasta wa wasu daga cikinsu yin hijira zuwa garin Nguru.

“Sauran yankunan da hamadar ta shafa sun hada da Tulo-Tulo da Bula-tura, garuruwa biyu masu iyaka da Jamhuriyar Nijar.

“Garuruwanmu na fuskantar hadarin bacewa,” in ji Aji.

Shugaban ya bayyana damuwarsa kan cewa nan ba da jimawa hamadar za ta shiga wani tapki mai matukar muhimmanci wajen samar da ruwa a yankin, idan ba a dauki matakan gaggawa na dakile hakan ba.

“ Dunkulewar yashin na barazana ga wani tabki mai ban sha’awa wanda ya ke samar da ruwa don anfanin gida da shuke-shuke musamman lokacin rani

“Wannan haɗari ne a fili kuma ga tattalin arzikin jama’ar mu, ma su noman rake, tumatur, rogo, gyada har ma da dankali.

“Idan aka bar tafkin ya bushe, za a samu matsalar tattalin arziki don mutane za su rasa aikin yi,” in ji shi.

Aji ya bayyana cewa kokarin da karamar Hukumar, gwamnatin jinar, da aikin Great Green Wall na gwamnatin tarayya da ma kungiyoyi masu zaman kansu suka yi ya yi kyau, amma bai samar da sakamakon da ake bukata ba.

Don haka shugaban ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar da wani gandu a yankin domin dakile yashin.

“Ina kira ga ofishin asusun kula da muhalli da gwamnatin tarayya da su ayyana dokar ta-baci kan kwararowar hamada a karamar hukumar Yusufari.

“Muna buƙatar gagarimin shirin dashen itatuwa don hana cigaba da kwarrowar hamadar,” inji shugaban.

Akan shirin karfafa aikin gona na jihar, ya yabawa gwamna Mai Mala Buni, bisa yadda ya ware injinan gona da sauran kayayyakin amfanin gona wa yankin.

“Kayan aiki, taki da ingantattun iri da aka baiwa manoman sun zo akan gaba, lokacin da manoma suka fi bukata.

“ Saboda rarraba kayan gonan a kan kari, za mu girbi amfanin gona mai yawa a wannan shekara, Insha Allahu .

“Saidai mun fuskanci ambaliyar ruwa da zaizayar kasa a bana saboda ruwan sama kamar da bakin kwarya, lamarin da ya kai ga rugujewar gine-gine tare da lalata amfanin gonaki.

“Mun kai tawaga daga gwamnati da SEMA inda gine-ginen suka ruguje, kuma muna sa ran taimako daga gare su nan ba da jimawa ba.(www.nannews.ng)(NAN)
NB/YEN/HMH
============
Mark Longyen ne ya gyara
08032857987


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *