Gwamnatin Tarayya za ta tallafawa jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa da N3bn
Gwamnatin Tarayya za ta tallafawa jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa da N3bn
Tallafi
Daga Muhammad Lawal
Birnin Kebbi, Agusta. 25, 2024 (NAN) Gwamnatin Tarayya ta ce za ta tallafa wa jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa da Naira biliyan 3 domin dakile illolin da ke tattare da ibtila’in.
Mista Wale Edun, Ministan Kudi Da Gudanar da Tattalin Arziki ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi ranar Lahadi.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa ministan ya yi magana ne jim kadan bayan ya duba wasu yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a Kebbi.
Edun ya ce: “A nan zan sanar da cewa Majalisar Tattalin Arziki ta kasa ta himmatu kuma ta dauki matakin tallafa wa daukacin jihohin tarayya da kuma babban birnin tarayya Abuja da Naira biliyan 3 domin rage radadin ambaliyar ruwa a bana.
“Hakan zai sanya Jihohi da yawa kamar Kebbi cikin kyakkyawan yanayi don samun damar shirya manoman su don gudanar da duk wani muhimmin aikin noman rani, wanda muke tsammanin za a samu nasara, da tsare-tsare da kuma aiwatar da su yadda ya kamata.
Hakan a cewarsa, zai kai ga samun nasara, tare da samar da hanyoyin samar da abinci a farashi mai sauki da rage hauhawar farashin kayayyaki da kuma kara daidaita tattalin arzikin kasar.
Ya bayyana aniyar shugaban kasa Bola Tinubu na taimaka musu wajen tabbatar da tsaro, juriya da ingantawa da kara yawan amfanin da suke samu da kuma zama kwandon abinci a Najeriya.
Shima da yake jawabi, Ministan Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sen. Atiku Bagudu, ya koka kan yadda ambaliyar ta shafi kananan hukumomi da dama fiye da yadda ya gani a lokacin da ya ziyarci yankunan kwanan nan.
Sai dai ya yaba da juriya da kwarin gwiwa da mutanen Kebbi suke da shi, inda ya ba da tabbacin za a zaburar da su don yin aiki mai kyau a lokacin noman rani.
Ministan ya ce, baya ga Naira biliyan 3, gwamnatin tarayya ta amince da wani Asusun Renewed Hope Infrastructure Fund wanda za a yi amfani da shi wajen samar da hanyar Badagry zuwa Sokoto da wasu hanyoyin.
“Mafi tsawan doguwar hanyar zai kasance ne a yankin jihar Kebbi. Hakazalika, ban ruwa da madatsun ruwa muhimman fasalin wannan sabon asusun samar da ababen more rayuwan ne.
“Don haka, za a fadada wuraren noman rani a duk fadin titin mai kilomita 1,000 kuma wani muhimmin bangare na tallafin noman zai kasance a Kebbi,” in ji shi.
A nasa bangaren, Gwamna Nasir Idris, ya roki gwamnatin tarayya da ta taimaka wa jihar duba da yadda ambaliyar ruwa ta mamaye filayen noman shinkafa da dama a jihar.
Ya ce: “Sun je Wacot Rice Mill da ke Argungu kuma sun ga abubuwa da kansu. Sun kuma ziyarci Matan Fada a garin Argungu inda suka ga yadda ambaliyar ta shafi gonakin shinkafa.
“Kebbi ita ce kan gaba wajen noman shinkafa a kasar nan, saboda jihar noma ce.”
Gwamnan ya yi kira ga ministocin biyu da su tattauna da shugaban kasar kan yadda za a taimaki jihar Kebbi, inda ya ce jihar na da karfin ciyar da al’umma baki daya da ma sauran su.
A cewarsa, a kokarin da gwamnatin jihar ke yi na bunkasa samar da abinci a kasa, gwamnatin jihar ta raba takin zamani, da itatuwa, famfunan tuka-tuka, da injinan fanfo na CNG ga manoma sama da 35,000 kyauta.
Sai dai ya ce damina ta zo da kalubale da dama, tare da lalata filayen noma.
“Don haka muna son gwamnatin tarayya ta kawo mana agaji domin noman shinkafa ta gabato.
“Tuni mun fara wayar da kan manoman mu cewa nan da nan bayan girbin damina, gwamnati a shirye take ta taimaka musu su koma noman rani,” in ji shi.
NAN ta ruwaito cewa tawagar sun kuma ziyarci cibiyar kula da ruwa ta Dukku a Birnin Kebbi. (NAN)( www.nannews.ng )KLM/MNA
Maureen Atuonwu ta gyara
Nabilu Balarabe ya fassara