Gwamnatin Jihar Yobe ta sanarda yiwuwar sabuwar ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 9
Gwamnatin Jihar Yobe ta sanarda yiwuwar sabuwar ambaliya ruwa a kananan hukumomi tara
Ambaliya
Daga Nabilu Balarabe
Damaturu, 11 ga Satumba, 2024 (NAN) Gwamnatin Jihar Yobe ta ce akwai yiwuwar samun sabuwar ambaliyar ruwa a kananan hukumomi tara na jihar a sakamakon shirin sakin ruwa daga madatsun ruwa na Dadinkowa da Lagdo.
Kananan hukumomin sun hada da Nguru, Bade, Karasuwa, Jakusko, Yusufari, Geidam, Tarmuwa, Bursari, Machina, Gujba da Fune.
Dokta Mohammed Goje, Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) ne ya yi wannan gargadin a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu ranar Talata.
Ya kara da cewa sakin ruwa daga madatsun ruwan guda biyu zai kara jefa mazauna yankunan cikin mawuyacin hali.
” Mazaunan wadannan garuruwan sun sha wahala sosai saboda ambaliyar da ta auku a yankin a baya, sakamakon mamakon ruwan da aka kwashe kwanaki ana yi.
“Yobe ta fuskanci ambaliyar ruwa tsakanin 15 ga Afrilu zuwa 9 ga Satumba 2024, wanda ya haifar da barna a kananan hukumomi da dama.
“Wannan shawara ta kasance gargadi saboda yiwuwar fitowar ruwa daga dam ɗin Dadinkowa, Kogin Hadeja-Jama’are, Kogin Kamodugu, da kuma dam ɗin Lagdo a Kamaru,” in ji Goje.
Sakataren zartaswar ya shawarci mazauna yankunan da su dauki matakan kariya da suka hada da kauracewa zuwa wurin da babu alamun ambaliya domin ceton rayuka da dukiyoyin su.
“Ku kasance kuna da masaniya ta hanyar sauraron bayanai akai-akai daga shugabannin alumma, kananan hukumomi da hukumar ba da agajin gaggawa ta jiha.
“Ku ci gaba da tuntuɓar gaggawa wurin hukumomi don shirin kota-kwana,” in ji shi.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa sama da gidaje 19,000 a cikin al’ummomi 432 ne ya zuwa yanzu ambaliyar ruwa ta shafa a jihar. (NAN) (www.nannews.ng)
NB/KLM
======
Muhammad Lawal ne ya gyara