NAN HAUSA

Loading

CDD ta tallafa wa mutane 120 da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri

CDD ta tallafa wa mutane 120 da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri

Spread the love

CDD ta tallafa wa mutane 120 da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri

Ambaliyar ruwa

Daga Hamza Suleiman

Maiduguri, Oktoba 15, 2024 (NAN) Cibiyar Dimokuradiyya da Ci Gaba (CDD), ta tallafa wa mutane akalla 120 da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri jihar Borno.

Kungiyar ta rarraba kayan abinci da ya kai na Naira N10 000 ga kowanne mutane 120 da iftila’in na ranar 9 ga watan Satumba ya shafa.

Da yake raba kayayyakin a Maiduguri, Daraktan CDD, Dokta Garuba Dauda, ​​ya ce an yi hakan ne domin yaba kokarin gwamnati na tallafawa wadanda abin ya shafa.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa wasu daga cikin kayayyakin da cibiyar ta raba sun hada da, shinkafa, spaghetti, da kuma man gyada.

“Duk da cewa ba zai yiwu a maye gurbin duk abin da aka rasa ba, wannan gudummawar na da nufin nuna goyon baya ga al’ummomin da abin ya shafa.

“Cibiyar tana da dadaddiyar sadaukarwa ga yankin Arewa-maso-Gabas tun 2012, tare da himma wajen magance matsalar rashin tsaro, adalci na rikon kwarya, da kuma matsalolin da suka shafi cin zarafin mata.

“Ya kamata mu zo da wuri, amma mun jira dama mu gana da Gwamna. A safiyar yau mun zo ne domin ziyarar jaje ga gwamnatin jihar da kuma ganin yadda za mu tallafa wa ayyukan agajin da ake ci gaba da yi,” in ji Dauda.

Daraktan ya kuma mikawa gwamnatin Borno kudi naira miliyan uku domin tallafawa wadanda abin ya shafa da sauran kayayyakin agaji.

“Babu wanda ya shirya don wannan bala’i, amma abunda muke ba da shi ne ya fi dacewa, ba kimar ba,” in ji darektan.

Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin, Binta Babagana, ta yaba da wannan karimcin na CDD, inda ta bayyana shi a matsayin “lokacin da ya dace da ceton rai”. (NAN) (www.nannews.ng)

 

HMS/AOM/KLM

 

==========

 

Abdullahi Mohammed/Muhammad Lawal ne ya gyara


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *