Gwamnatin Borno za ta rufe makabartu biyu saboda da cunkoso

Gwamnatin Borno za ta rufe makabartu biyu saboda cunkoso

Makabarta
Daga Nabilu Balarabe
Damaturu, Aug 24, 2024 (NAN) Gwamnatin Jahar Borno ta ce a ranar 1 ga Satumba za ta rufe manyan makabartu biyu da suka cika a Birnin Maiduguri don guje wa barkewar annoba.

Makabartun sun hada da Makabartar Musulmai ta Gwange ta da ke Hanyar Bama da Makabartar Kirista da ke tsohuwar GRA.

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da ke dauke da sa hannun Alhaji Mohammed Abubakar, Babban Sakataren Hukumar Harkokin Addinai ta jihar a ranar Jumma’a a Maiduduguri.

Ya ce gwamnatin ta samar da sabbin makabartu biyu da suka hada da Makabartar Dalori ta kan Hanyar Bama ga Musulmai, da kuma Makabartar alumar Kirista Mai Matsanancin Tsaro da ke kan Hanyar Baga.

Abubakar ya ce samar da sabbin makabartun ya biyo bayan bukatar yin hakan da ga alummai daba daban na jihar.

Babban Sakataren ya kara da cewa gwamnati za ta ci gaba da bude sabbin makabartu a fadin jihar a duk inda akwai bukatar yin hakan.

Ya ce tuni gwamnatin ta sayo motocin guda shida da za ta bayar da su ga alumar Musulmi da na kirista don daukan gawawwaki.(www.nannews.ng)(NAN)NB

Rubutawa: Nabilu Balarabe

An ceto daliban likitanci 20 da akayi garkuwa da su

An ceto daliban likitanci 20 da akayi garkuwa da su

Ceto
Daga Emmanuel Anstwen
Makurdi, Aug 24, 2024 (NAN) Hukumar Yan Sanda a jihar Benue ta tabbatar da sakin daliban jamio’in Maiduguri da Jos da aka sace a jihar da ke Arewa Maso Tsakia a ranar 15 ga Augusta.

Jamiin Yada Labaru na Yan sandan, Mista Sewuese Anene, ne ya tabbatar sakin daliban wa kampanin Dillancin Labarun Nageria (NAN) a Makurdi ranar Jumma’a.

Kamfanin Dillacin Labarai Na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa daliban an sace su ne a garin Oturkpo yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Enugu don taron shekara-da-shekara na gamayyar daliban likitanci na katolica ( FECAMDS).

Rahoton ya kara da cewa wani jamiin kiwon lafiya da ke tare da daliban shima an sace shi.

Sai dai Anene bai bada Karin haske ga ceton daliban da akayi ba.

“ An sako wadanda aka kama. Za‘a bada karin bayani a gobe ( Azabtar) da safe,” ya ce.

Sako daliban na zuwa ne kwana biyar bayan Shugaban Yansandan Nigeria, Mista Olukayode Egbetokun, ya turo zaratan Yansanda zuwa Benue, ya kuma ba wa Shugaban Yansandan jihar umurnin ya ta fi Oturkpo.

NAN ta gano cewa wata hadakar jamian tsaro bisa jagorancin Mai Bawa Shugaban Kasa Shawara Akan Harkokin Tsaro ne ta ceto daliban.(www.nannews.ng)(NAN)AEB/ETS
Fassara daga Nabilu Balarabe