Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 20, ta raba 2,000 da gidajensu a Yobe
Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 20, ta raba 2,000 da gidajensu a Yobe
Ambaliyar
Daga Nabilu Balarabe
Gashua (Yobe), 7 ga Satumba, 2024 (NAN) Mutane 20 ne suka mutu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a karamar hukumar Bade ta jihar Yobe tun farkon watan Agusta, in ji shugabanta, Alhaji Babagana Ibrahim.
Ibrahim ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, (NAN) ranar Juma’a a Gashua cewa yawancin wadanda suka mutun sun makale ne a karkashin baraguzan gidajen laka da suka ruguje.
Ya ce ambaliyar ta lalata gidaje sama da 10,000 kuma ta yi awun gaba da filayen noma a cikin ya Kuna kusan 200.
Shugaban ya lissafa kauyukan da bala’in ya fi shafa da suka hada da Misilli, Lawan Musa, Dagona, Dala, Katuzu da Sabongarin Gashua.
Ya ce mutane 2,000 da ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu suna samun mafaka a sansanoni uku da a ka Taba da a Gashua.
Ya lissafa sansanonin a da suka hada da Goodluck, Zango 2 da Babuje.
Ibrahim ya ce majalisar karamar hukumar tana kokarin ciyar da ‘yan gudun hijirar abunci tun lokacin da suka zo sansanonin.
Ya ce kwanan nan Sanata Ahmed Lawan, tsohon shugaban majalisar dattawa ya bayar da gudummawar naira miliyan 10 ga wadanda abin ya shafa, yayin da gwamnatin jihar tuni ta fara raba kayan abinci ga wadanda abin ya shafa.
Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta kai dauki ga wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su wadanda a kullum yawansu ke karuwa.
“ Mutane na cikin halin kaka-ni- kayi saboda girman wannan ibtila’in da ya faru kuma ya sha karfin karamar hukumar Bade.
“Don haka ne nake kira ga gwamnatin tarayya ta hannun Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), da ta kawo mana agaji, ganin yadda ’yan gudun hijira ke ci gaba da karuwa,” in ji shi.(www.nannews.ng) (NAN)
NB/ETS