NAN HAUSA

Loading

Yadda mace yar shekara 40 ta sawa kanta wuta a Jigawa 

Yadda mace yar shekara 40 ta sawa kanta wuta a Jigawa 

Spread the love

Yadda mace yar shekara 40 ta sawa kanta wuta a Jigawa

 

 

 

Kuna

Daga Muhammad Nasir Bashir

 

Dutse, Aug. 23, 2024 (NAN) Wata mace me shekaru 40 a Karamar Hukumar Guri dake Jahar Jigawa ta bankadawa kanta wuta sanadiyar bakin cikin sakin da mujin ta ya yi mata.

 

Jami’i mai magana da miryan rundunar yan sandan jahar, DSP Lawan Shiisu ne ya tabbatar da mummunan labarin a wani jawabi da ya fitar a ranar Juma’a.

 

A cewar Shiisu, macen dake zama a kauyen Malam, ta yi amfani da man fetur wajen sawa kanta wuta.

 

“A ranar Alhamis misalin 7: 40 na safe ne hukumar yan sandar ta samu mummunan labarin me ban tausayi daga karamar hukumar Guri, cewa mace yar shekaru 40 a kauyan Malam ta kuza man fetur a jikinta da kanta a wajen gari, sanadiyar hakan ta samu mummunar kuna.

 

“Take da samun bayanin, kwararrun yan sanda dake hedikwatar ofishin Guri suka bazama zuwa inda hadarin ya faru.

 

“Jami’an yan sandan sun dauki gawar macen dake kone zuwa asibiti daga bisani kuma suka mika ta zuwa wajen iyalan  ta domin yi mata sutura,” cewar Shiisu.

 

Mai magana da miryan yan sanda ya kara da cewa hukumar ta su take ta fara bincike dan gano gaskiyar lamarin, du da an san marigayiyar ta shiga mummunan yanayin bakin ciki da damuwa a watannin baya, sanadiyar mutuwar auren ta.

 

Ya kara da cewa Kwamishinan yan sanda na Jahar Jigawa, Ahmadu Abdullahi, ya shawarci Jama’a da su rika mika lamuransu ga ubangiji dan samun mafita.

 

Abdullahi ya jaddada shawaran da cewa mutane su kuma rika neman shawaran magabata a cikin yanayin kunci do damuwa  domin gujewa fadawa yin aika aika.

(NAN) (www.nannews.ng)

 

MNB/SH

 

=======

 

edita Sadiya Hamza

 

Fassara daga Abdullahi Mohammed/Bashir Rabe Mani

 


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *