Hukumar zaɓen Malawi ta kudiri yin zaɓen 2025 da sabun na’urar kimiya
Hukumar zaɓen Malawi ta kudiri yin zaɓen 2025 da sabun na’urar kimiya
Zaɓe
Lilongwe, Aug. 22, 2024 (Xinhua/NAN) Hukumar zaɓen kasara Malawi (MEC) ta aje sabuwar na’urar kimiya (Electoral Management Devices (EMDs), wajan dai dai ta tsarikan hanyoyin babban zaɓen kasar da za’yi a watan Satumba na shekarar 2025.
Jami’iin da ke magana da yawun hukumar, Sangwani Mwafulirwa, ya sanar da cewa hukumar ta sayo na’urorin EMDs kimanin 6,500 daga wani kamfanin da ke zaune a kasar Netherlands me suna (Smartmatic International Holdings B.V. Company).
Sabuwar na’urar kimiyar zata maye gurbin na’ura me dauke da bayanan mutane na registan zaɓe wadda ake kira (Biometric Voter Registration System), wanda aka yi amfani da ita a babban zaɓen kasar na shekarar 2029, da kuma zaɓen nanata kammala zaɓen shugaban kasa.
Ana sa ran Kwamishinan zaɓen kasar zai yi amfani da sabuwar na’urar wajen rajistar kuri’u da tsare tsaren masu bukatar canjin wajan yin zaɓe da kuma ziyarce ziyarce duba wajen yin rajistar zaɓe.
Mwafulirwa yace gabatar da sabuwar na’urar MEDs na cikin tsarin dabarun hukumar MEC ta wajen bunkasa tsarin hanyoyin gudanar da babban zaɓen kasar.
(Xinhua/NAN)(www.nannews.ng)
UMD/HA
========
Editoci sune
Ummul Idris/Hadiza Mohammed-Aliyu
Fassara daga Abdullahi Mohammed/Bashir Rabe Mani