‘Yan sanda na bincike kan harin da aka Kaiwa tawagar Malami a Kebbi
Daga Ibrahim Bello
Birnin Kebbi, Satumba 2, 2025 (NAN) Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, ta fara gudanar da bincike kan harin da aka kaiwa ayarin motocin tsohon ministan shari’a kuma babban lauya Abubakar Malami (SAN), a Birnin Kebbi.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa an kaiwa ayarin motocin Malami hari ne a ranar Litinin, a lokacin da suke dawowa daga ziyarar jaje a babban birnin jihar.
Malami ya fice daga jam’iyyar APC ne a ranar 2 ga watan Yuli, sannan ya koma jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
Bayan wani taron gaggawa da jami’an tsaro suka yi da jami’an tsaro, kwamishinan ‘yan sanda, Mista Bello Sani, ya tabbatar da cewa ba a kama kowa ba.
“Mun fara bincike kan harin, kuma ba a kama wani mutum ba tukuna, ya kara da cewa Gwamnan Kebbi, ya kira wannan taro ne domin duba abubuwan da suka shafi tsaro,” in ji Sani.
Sani ya kara da cewa, al’amarin ya faru a kewayen yankin GRA da suka shafi ‘yan jam’iyyun siyasa, wadanda ke da alaka da saba ka’idojin yakin neman zabe na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
Kwamishinan ya bayyana cewa, za a gayyaci shugabannin jam’iyyun siyasa tare da gargadinsu akan sabawa ya ka’idojin zabe.
Ya jaddada cewa za a dauki matakai, da nufin hana afkuwar tashin hankali yayin da zaben da ke kara kusantowa.
Kwamishinan ya kuma bukaci shugabannin siyasa a Kebbi, da su kwantar da hankalinsu da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar. (NAN) (www.nannews.ng)
IBI/KTO
======
Fassarar Aisha Ahmed