Yan kasuwa sunyi alwashin bada gudumawa wajen bunkasar tattalin arzikin Afrika
Yan kasuwa sunyi alwashin bada gudumawa wajen bunkasar tattalin arzikin Afrika
Kasuwanci
Daga Aderogba George
Abuja, Aug. 24, 2024 (NAN) Taron shugabannin kasuwanci da zuba jari na Afrika (ABLIS) 2024 da aka shirya gudanar wa a birnin Kigali na kasar Rwanda, ya ce taron zai ba da gudunmawa sosai wajen mayar da Afirka ta zama cibiyar kasuwanci ta duniya.
Shugaban ABLIS, Shirley Hills, ce ta bayyana haka a taron dabarun hadin gwiwar da aka yi a Abuja ranar Alhamis, cewa taron zai gudana a tsakanin 7 ga Oktoba zuwa 12 ga Oktoba.
Hills ta ce shirin na kwanaki shida zai mayar da hankali ne kan inganta gasa tsakanin ‘yan kasuwa a Afirka.
A cewar ta, taron zai samar da wani tsari na inganta harkokin kasuwanci a Afirka da hadin gwiwar tattalin arziki da ba a taba yin irinsa ba a Afirka, da kuma yadda za a bunkasa tattalin arzikin nahiyar.
Ta ce taron zai ba da dama ga shugabannin ‘yan kasuwa na Afirka su ba da labarin yadda suke tafiyar da harkokin kasuwanci da wadata.
“Taron zai yi tasiri a kan shugabannin siyasar nahiyar musamman kan yadda za su bunkasa hanyoyin samun ci gaban tattalin arzikin kasar su (GDP), da kuma bunkasa tattalin arzikin Afirka.
“Taron da ke tafe zai nuna mahimmancin himma tare da jaddada bukatar ‘yan kasuwan Afirka su rungumi kyawawan dabi’u a duniya tare da bunkasa kasuwancin tsakanin nahiyoyi.
“Muna kawo sauye-sauyen harkokin kasuwanci a duniya da hadewar kasashen Afirka saboda muna son ‘yan Afirka su yi kasuwanci da ‘yan Afirka don Afirka.
“Yana da matukar muhimmanci mu sanya tsarin sauye-sauyen harkokin kasuwanci a duniya, da tabbatar da cewa kasuwancin Afirka sun samar da ingantattun ayyuka na duniya,” hills ta kara da cewa.
Ta kuma yi kira ga Najeriya da ta yi amfani da tsarin da taron ya samar, inda ta kara da cewa kasar na da tarin ribar da za ta samu daga taron.
Mista Paul Abbey, abokin huldar dabarun ABLIS, ya ce kamata ya yi Najeriya ta yi amfani da damar taron don tallata arzikinta na albarkatun kasa,.
“Tabbas ta hanyar hadin gwiwa da kuma bayyana irin karfin da Najeriya ke da shi, nahiyar za ta ci moriyarta, ita ma Nijeriya za ta amfana, muna da albarkatun kasa da yawa da ya kamata a yi kasuwa a can.
“ABLIS yana shirye don ƙirƙirar dandamali don bayyani; ‘Yan kasuwa da yawa za su san cewa Najeriya na da albarkatun kasa; za su hada kai da gwamnati don kara inganta kasuwancin kasa da kasa,” in ji shi.
Mista Obinna Simon, wani abokin hadin gwiwa, ya jaddada bukatar yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen Afirka, don bunkasa karfin kasuwancin su, yana mai cewa, babu wata kasa da za ta iya tsayawa kanta.
Ya ce hadin gwiwar ya ba da dama ga kasashe su shiga harkokin kasuwanci na wasu kasashe, yana mai cewa yana taimakawa wajen musayar ra’ayi.
“Hadin gwiwar wani mataki ne na ci gaban kasa, zai samar da damammaki masu yawa ga matasa, kere-kere da damar saka hannun jari”, in ji Simon. (NAN)(nannews.ng)
AG/KUA
======
Uche Anunne ne ya gyara
Fassarawa: Abdullahi Mohammed