Shettima ya goyi bayan laccar tsaro ta yankin Sahel da NAN zata shirya
Shettima ya goyi bayan laccar tsaro ta yankin Sahel da NAN zata shirya
Tsaro
Daga Salisu Sani-Idris
Abuja, Satumba 2, 2024 (NAN) Mataimakin shugaban kasa Kashim
Shettima a ranar Litinin ya yi kira da a kara bayar da tallafi
ga lacca ta kasa da kasa kan rashin tsaro a yankin Sahel.
Shettima ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin
shugabannin kamfanin dillancin labarai ta Najeriya (NAN) a
karkashin jagorancin Manajan Daraktanta, Malam Ali Muhammad Ali,
a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Mataimakin shugaban kasar ya jaddada muhimmancin hada kai,
inda ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu na matukar sha’awar
sha’anin tsaro a Najeriya, kuma ba zai dauki matakin da wasa ba.
Shettima ya kuma yi kira da a yi kokari na shiyya-shiyya da na
gamayya don magance matsalar rashin tsaro a yankin Sahel na
yammacin Afirka.
Ya lura cewa yanayin tsaro a yankin Sahel yana da matukar tasiri
ga Najeriya da kuma kasashe makwabta.
Lakca ta kasa da kasa da NAN ke shirya ya dace sosai, musamman
kan batun rashin tsaro a yankin Sahel.
“Matsalar tsaro a cikin al’umma abu ne da shugaban kasa ke
matukar sha’awa kuma ba ya daukar matakin da sauki,” inji shi.
Shettima ya bayyana kwarin guiwar sakamakon taron.
Ya ce"Na yi imanin cewa tare da kimar mutanen da za su yaba da
lacca, za ku fito da ra'ayoyi da dama kan yadda za a magance
matsalar rashin tsaro a yankin Sahel ta hanyar da ta dace."
Tun da farko, Ali ya shaida wa mataimakin shugaban kasa
Shettima cewa, taken taron shi ne "Rashin tsaro a yankin
Sahel (2008-2024): Rarraba kalubalen Najeriya - Asali, Illoli da hanyoyin zabi".
Ya sanar da cewa, wanda zai jagoranci laccar da za a yi a ranar
25 ga watan Satumba, shi ne Mohamed Ibn Chambas, tsohon
shugaban hukumar ECOWAS.
A cewar sa, taron wani bangare ne na kokarin da NAN ke yi na
fadada rawar da ta ke takawa fiye da yada labarai don ba da
gudummawa sosai wajen tattaunawa kan kasa da magance matsalolin.
"NAN ta shirya lacca ta farko ta kasa da kasa a matsayin
wani bangare na rawar da kafafen yada labarai ke takawa na
fadada iyakokin ilimi da samar da hanyoyin magance matsaloli,"
in ji Ali.
Ya zayyana tsare-tsare da dama da ke da nufin inganta isar
da sahihancin NAN, ciki har da bullo da yada shirye-shiryen
yare.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Daraktan
gudanarwa na NAN, Malam Abdulhadi Khaliel; Daraktan ayyuka
na musamman, Muftau Ojo; Mataimakin Darakta na NAN kafofin yada labarai na zamani,
Ismail Abdulaziz; da Sakatariyar hukumar, Ngozi Anofochi.
(NAN)(www.nannews.ng)
SSI/AMM
======
Abiemwense Moru ne ta gyara