Tsohon mai magana da miryan yan sanda na neman taimakon N25m na dashin koda
Tsohon mai magana da miryan yan sanda na neman taimakon N25m na dashin koda
Koda
Daga Moses Omorogieva
Lagos, Aug. 22, 2024 (NAN)Tsohon mai magana da miryan yan sanda na rundunar Jahar Legas, kuma matemakin Kwamishinan Yan sanda, Chike Oti, wanda yake fama da chutar koda, yayi kira da yan Najeriya da su temaka masa da gudunmawar kudi Naira milyan N25 dan yin dashin koda.
Bayani ya fito ne a wata sanarwa da Oti ya fitar wacce yamika wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Alhamis a birnin Legas.
A cewar majinyacin, binciken da akayi masa a dan tsakanin nan, ya tabbatar da yana dauke da cutar kodar a matakin hawa na biyar mafi hadari.
“Ya ku yan u wanna mazanku da matanku, sunana matemakin kwamishinan yansanda Chike Godwin Oti, wanda akayimin canjin wajan aiki zuwa rundunar yansanda dake kula da harkokin jiragan kasa hedikwatar ta dame Ebutte Meta a jahar Legas,” a cewar.
“Inna so na sanar daku cewa anyi min gwajin cutar koda me matakin hawa nabiyar (kidney failure) mafi hadari, wanda ake masa suna da cewa matakin karshen cutar koda.
”Ya kuma zamo da nau’iin hawan jini mafi hadari a asibitin Lagoon dake unguwar Lagoon Bourdillion na Ikoyi, dake birnin Legas.
“Shawarwarin kwararru shine yin wankin koda na (hemodialysis) so biyu a mako shine kadai dama ta na kasancewa a raye kafin samun kuɗin dashin kodar da ake neman miliyan N25.
“A karin kaina kawo yanzu na kashe kuɗin da kimaninsu yakai miliyan 3.5 acikin mako daya da na kwanta a wannan asibitin.
“A dadin kuɗin da zai sa na kasance a raye a wuce samu na nesa ba kusa ba. A nan ne nake mika kokon bara na zuwa ga yan uwana maza da mata da samun ganin cin nasara wajen yakar wannan cutar,” cewar Oti.
Ya yi bayanin cewar me san ya temakesa na iya aikawa da kudi ta asusun ajiya kamar haka:
Acct. No: 2016631487, Bank: UBA PLC, Name: CHIKE OTI, Phone No: 07065246927. (NAN) (www.nannews.ng)
MIO/CHOM/IKU/
=============
Editoci sune:
Chioma Ugboma/Tayo Ikujuni
Fassara daga
Abdullahi Mohammed/Bashir Rabe Mani