Sultan ya umurci musulmi da su duba watan Sha’aban
Sultan ya umurci musulmi da su duba watan Sha’aban

Sha’aban
Daga Muhammad Nasiru
Sokoto, Janairu 28, 2025 (NAN) Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Alhaji Sa’ad Abubakar, ya umurci Musulmi da su fara duban jinjirin watan Sha’aban 1446H daga Laraba .
Umarnin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na Majalisar Sarkin Musulmi Farfesa Sambo Junaidu ya fitar a Sokoto ranar Talata.
“Ana sanar da al’ummar musulmi cewa ranar Laraba 29 ga watan Janairu, daidai da 29 ga watan Rajab 1446 Hijira, ita ce ranar da za a duba jinjirin watan Sha’aban na shekarar 1446 bayan hijira.
“Saboda haka, an bukaci musulmai da su fara neman jinjirin watan Sha’aban a ranar Laraba kuma su kai rahoton ganinsa ga gunduma ko kauye mafi kusa don sadarwa ga Sarkin Musulmi,” in ji shi.
Sarkin Musulmi ya yi addu’ar Allah ya shiryar da dukkan musulmi yayin da suke gudanar da ayyukansu na addini.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa watan Sha’aban shi ne wata na takwas a kalandar Musulunci kuma shi ne watan karshe kafin watan Ramadan. (NAN) (www.nannews.ng)
BMN/MAM/BHB
Edited by Modupe Adeloye/Buhari