Sultan ya bukaci a yi addu’ar Allah ya kawo mana cigaba a Najeriya

Sultan ya bukaci a yi addu’ar Allah ya kawo mana cigaba a Najeriya

Spread the love

Sultan ya bukaci a yi addu’ar Allah ya kawo mana cigaba a Najeriya

Addu’a

Daga Habibu Harisu

Sokoto, June 7, 2025 (NAN) Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA), Alhaji  Sa’ad Abubakar, ya bukaci sarakunan gargajiya da su yi wa Nijeriya addu’a.

Ya yi wannan roko ne bayan da ya jagoranci addu’a ta musamman bayan Sallar Juma’a , wanda Babban Limamin Masallacin Sultan Bello, Sheikh Bello Akwara ya gabatar a ranar Juma’a a Sakkwato.

Abubakar ya ce shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci shugabannin addini da na gargajiya tare da kungiyoyin addini da su rika gudanar da addu’o’i a kodayaushe domin magance kalubalen da kasar ke fuskanta.

Ya yi nuni da cewa, dukkan al’ummomi na fuskantar kalubale na musamman, kuma yayin da ranar dimokuradiyya ke gabatowa, ya kamata ‘yan Nijeriya su yi addu’a domin ci gaban kasa, da ingantattun manufofi, da zaman lafiya.

Ya kuma bukaci al’ummar musulmi da su ci gaba da yi wa shugabanni addu’a, yana mai jaddada cewa addu’a ce kawai za ta iya tallafa wa bukatun kowace al’umma.

Sarkin Musulmi ya bukaci sarakunan gargajiya da kungiyoyin addini da daidaikun jama’a da su shirya irin wannan addu’o’in a fadin kasar nan domin samun zaman lafiya da kuma shawo kan kalubalen da ake fuskanta a halin yanzu.

Ya bayyana godiya ga hukumomin tsaro bisa ci gaba da kokarin da suke yi na tabbatar da tsaro da walwalar ‘yan kasa a fadin kasar nan.

“Mun san gwamnati na yin iya kokarinta don rage wahalhalu, amma a fili har yanzu ana bukatar karin kokari.

“Mutanen mu, musamman a Arewa, suna fuskantar wahala sosai, dole ne shugabanni su kara daukar matakai masu tsauri don magance wadannan matsalolin,” inji shi.

Abubakar ya godewa musulmi bisa jajircewar da suka yi na yada kyawawan dabi’u na Musulunci tare da karfafa imani da ci gaba da ganin an shawo kan kalubalen da Najeriya ke fuskanta.

A lokacin da yake taya al’ummar Musulmi murnar Sallah Idi Kabir, ya yi addu’ar Allah ya dawo da su lafiya, ya kuma bukaci su yi wa Najeriya da shugabanninta addu’a. (NAN) (www.nannews.ng)

HMH/KTO

=========

Edited by Kamal Tayo Oropo


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *