SOKAPU ta kara kaimi wajen neman kirkiro jihar Gurara
SOKAPU ta kara kaimi wajen neman kirkiro jihar Gurara
Jiha
By Hussaina Yakubu
Kaduna, Maris 5, 2025 (NAN)Kungiyar Kudancin Kaduna (SOKAPU) ta kara kaimi wajen tuntubar juna da fafutukar ganin an samar da jihar Gurara, tare da yin amfani da shawarar da majalisar wakilai ta yanke na sake kirkirar sabbin jihohi.
Domin karfafa yunƙurin ta, SOKAPU ta kafa wani kwamiti mai ƙarfi a ƙarƙashin jagorancin Mista Mark Jacob don daidaita shawarar tare da shigar da manyan masu ruwa da tsaki a matakin jihohi da na ƙasa.
A wani taron manema labarai, shugaban kungiyar SOKAPU, Solomon Tabara, ya bayyana cewa kungiyar ta samu goyon bayan ‘yan majalisa da wasu masu fada aji.
Ya yi watsi da ikirarin cewa Gwamna Uba Sani na adawa da matakin, inda ya gabatar da hujjojin da ya nuna goyon bayansa a baya kan wannan kudiri na sabuwar jihar Kaduna.
“Da’awar cewa gwamnan yana adawa da jihar Gurara ba shi da tushe. Bayanan da ke akwai sun nuna ba haka ba.
“Muna kira ga mutanenmu da su kasance masu haɗin kai kuma kada a yaudare su da labarun ƙarya,” in ji Tabara.
Ya ce jihar Gurara ta kunshi kananan hukumomi 12, inda take alfahari da fadin kasa fiye da jihohin da ake da su.
A cewar Tabara, jihar da ake shirin yi na da arzikin noma da ma’adanai, wanda hakan ke kara inganta tattalin arzikinta.
Ya ce, “A yayin da majalisar wakilai ta sake bude kafar, SOKAPU ba ta bar wani abu ba don tabbatar da cewa shawarar ta ta cika ka’idojin tsarin mulki.”
Tabata ya kuma nuna kwarin gwiwar cewa burinsu na dq ya dade ya kusa aiwatuwa.(NAN)(www.nannews.ng)
HUM/BRM
=========
Edited by Bashir Rabe Mani