Sojoji sun kama wani mutum bisa zargin karkatar da injinan gona a Yobe
Sojoji sun kama wani mutum bisa zargin karkatar da injinan gona a Yobe
Kame
Daga Nabilu Balarabe
Damaturu, Aug 27, 2024 (NAN) Dakarun Sojoji na Forward Operations Base (FOB) a Yobe sun kama wani mutum dan shekara 43 da haihuwa da injinan shuka guda 19.
Injinan na daga cikin kayayyakin gona da gwamnatin jihar ta rabawa manoma a baya-bayanan a karkashin shirinta na bunkasa noma.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da Mai Bada Shawara Na Musamman ga Gwamna Mai Mala Buni, Brig.-Gen. Dahiru Abdulsalam maimurabus ya fitar.
Ya ce an kama mutumin ne da misalin karfe 12:10 na safiyar ranar Talata bayan ya boye injinan a cikin wata motar safa da ke kan hanyar Potiskum zuwa Gombe.
“Yau, da misalin karfe 00:10 na safe, sojojin FOB Potiskum sun kama wani mutum da injinan shuka iri 19.
“Kayan, wadanda ake zargin an fitar da su ne domin shirin karfafa ayyukan noma na jihar Yobe, an boye su ne a cikin wata motar bas mai dauke da kujeru 18 mai launin shudi mai lamba: KTG 449 YG,” in ji Abdulsalam.
Ya Kara da ce wanda ake zargin bai iya bayar da wata hujjar da ke nuna cewa shi ya ci gajiyar shirin ba.
“Maikayan ba shi da wata takadda da ke nuna cewar gwamnati ce ta bashi kayan ko ta ba wasu.
“Wanda ake zargin wanda ya fito daga Jigawa ya ce ya sayi kayan ne a hannun wani Alhaji Babaji mai lamba 08032837370 a Damaturu akan kudi N50,000.00 kowanne.
“Ya bayyana cewa zai kai kayayyakin Dutse a jihar Jigsawa don ya sayar,” inji shi.
Abdulsalam ya ce wanda ake zargin da kayayyakin da aka kwato za a mika su ga hukumar tsaro ta NSCDC domin gurfanar da su a gaban kuliya.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Buni ya umarci jami’an tsaro da su kama duk wanda su ka samu yana kokarin fitar da injinan da ga jihar.(NAN) (www.nannews.ngg)
NB/SH
=====
Sadiya Hamza ta gyara