Shugaba Tinubu ya karrama Bill Gates

Shugaba Tinubu ya karrama Bill Gates

Spread the love

Shugaba Tinubu ya karrama Bill Gates

Karramawa

Daga Salif Atojoko
Abuja, Yuni 4, 2025 (NAN) Shugaba Bola Tinubu, ya yaba wa Bill Gates, wanda ya kafa Kamfanin Na’ura Mai Kwakwalwa ta Microsoft kuma shugaban gidauniyar Bill Gates tare da shi lambar kwamandan Oda ta Tarayyar Tarayya (CFR).

Shigana Tinubu ya karramash da lambar yabon ta kasa bisa yadda ya zaburar da shugabanni a duk duniya wajen ci gaba da daukaka tare da taimakon talakawa da marasa galihu.

Shugaban ya lura da irin ayyukan da
fitaccen mai bayar da agajin Gates ke yi a fannin kiwon lafiyar mata, noma da bincike kan cututtuka.

Tinubu ya godewa Gates saboda samar da shugabanci na duniya wanda ya ba da fifiko wajen inganta rayuwa da amincin talakawa da marasa galihu.

“A yau, zan so in yi yarayya da Gates cikin  farin ciki da girmamawa da kuma saninsa daya daga cikin manyan mutane a duniya.

“Abin ba kawai in gode ma Bill Gates ba, saboda sadaukarwar sa ga bil’adama wadda ke da matukar ban mamaki.

“Wannan abin zaburarwa ne ga shugabanni a duk duniya, gami da wanda ke gaban ku. Ya kara da cewa

“Na gode maka matuka, abu ne mai girma na karrama ka a matsayinka na Shugaban Tarayyar Najeriya.”

Gates, a martanin da ya mayar, ya ce ya samu karramawa ne da kyautar CFR da shugaban kasa ya yi.

Yace “na yi matukar farin ciki da samun karramawa ga kaina da kuma tawagar da ta yi fice a gidauniyar, tun da farko manufar gidauniyar ita ce tallafa wa harkar kiwon lafiya a Najeriya.

“Najeriya na da wasu buri masu kyau na inganta lafiya, kuma mutane uku a nan a yau sune manyan gwanayen wannan harka.

“Tabbas, shugaban kasa yana ba da fifiko kan kiwon lafiya. Munyi aiki da Ministan Lafiya da Cigaban Jama’a, Farfesa Muhammad Pate, don
magance manyan kalubale,
ciki har da ci gaba mai ban mamaki game da cutar shan inna.

“Acikin shekaru 25 da muka yi a Najeriya, mun samu nasarori da dama, kamar yadda aka ambata, yawan mace-macen kananan yara ya ragu,
kuma hakan ya faru ne saboda an samu sabbin alluran rigakafi don bunkasa kokarinmu.”

Ya bayyana cewa kokarin kawar da cutar shan inna na daya daga cikin mafi tsauri da Gidauniyarsa ta yi.

Ya kara da cewa “an koyi abubuwa da yawa, kuma an gina haɗin gwiwa tare da cibiyoyin gargajiya.”

Ya ce tuni gidauniyar ta fitar da allurar rigakafin cutar HPV domin rage mace-macen mata 7,000 a duk shekara sakamakon cutar kansar mahaifa,
kuma allurar rigakafin da ‘yan mata masu shekaru 9-14 suka dauka na iya ba su kariya ta rayuwarsu.

“Najeriya ta samu sakamako mai kyau fiye da kowace kasa wajen samar da allurar rigakafin ga yara mata,” in ji shi.

Gates ya shaidawa shugaba Tinubu cewa ya himmatu wajen rage rashin abinci mai gina jiki da yada alluran rigakafin da ka iya kawo karshen zazzabin cizon sauro a Najeriya.

Ya kara da cewa “wasu daga cikin manufofinmu za su zama masu buri mai nisa; misali, nan da shekaru ashirin masu zuwa, muna fatan kawar da
cutar zazzabin cizon sauro.”

Gates ya tabbatar wa shugaban Najeriyar kan ci gaba da jajircewarsa na inganta harkar lafiya a Najeriya, da nufin zuba jarin dukiyarsa a wannan fanni nan da shekaru 20 masu zuwa.

Tun da farko, Farfesa Pate ya ce karrama Gates ya dace sosai, duba da yadda ya dade yana taka rawa wajen ci gaban Najeriya.

Yace “abokin Bill Gates, Alhaji Aliko Dangote, yana aiki tare da shi wajen kawo sauyi a fadin kasar nan.

“Tun daga wancan lokacin har zuwa yanzu, gidauniyar Gates da sauran gurabun sun kashe sama da dala biliyan biyu na jarin ta a fage daban-daban da suka shafi al’ummarmu kai tsaye, walau ta fuskar lafiya, noma, ko tattalin arzikin zamani.

“Mahimmancin lokacin da ya shigo Arewacin Najeriya, an fuskanci kalubale na rigakafi, mutane sun ki saboda jahilci, kuma tare da Mista Gates da Alhaji Aliko, sun hada dukkan kwamitin sarakunan gargajiya,” in ji shi.

Pate ya ce babban goyon bayan gidauniyar Bill da Melinda Gates ta kawar da cutar shan inna a Najeriya. (NAN)(www.nannews.ng)
SA/MUYI

========
Muhydeen Jimoh ne ya gyara 


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *