Shettima ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya wajen Jana’izar mahaifiyar marigayi Yar’Adua
Shettima ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya wajen
Jana’izar mahaifiyar marigayi Yar’Adua
Shettima
Daga Salisu Saniidris
Abuja, Satumba 4, 2024 (NAN) Mataimakin shugaban kasa Kashim
Shettima a ranar Talata ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya
domin halartar jana’izar mahaifiyar marigayi shugaban kasa, Umaru Yar’Adua.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa Hajiya Binta (Dada)
Yar’Adua mai shekaru 102 ta rasu ne a ranar Litinin a Katsina kuma aka binne
ta a can ranar Talata.
Da yake magana a madadin shugaban kasa Bola Tinubu, Shettima ya bayyana
matukar alhinin al’ummar kasar dangane da rasuwar Hajiya Binta.
NAN ta ruwaito cewa marigayiyar ta kuma kasance mahaifiyar marigayi tsohon
shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya, Janar Shehu Yar’adua.
Ya ce rasuwar Hajiya Binta rashi ne ba ga dangi ko jihar Katsina kadai ba, har
ma da al’ummar kasa baki daya.
Ya yaba wa marigayin, yana mai bayyana ta a matsayin "mace mai kyan gani kuma
kyakkyawa".
“Rashin Hajiya Binta ya shafi al’ummar kasar baki daya. Muna
nan don jajantawa 'yan uwa kan wannan babban rashi. Ita ce
mahaifiyarmu kuma kakarmu.
“Allah ya jikanta da rahama, ya saka mata da gidan Aljannah.
“Allah ya baiwa gwamnati da iyalai da al’ummar jihar Katsina
karfin gwiwar jure wannan rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba,”
inji shi.
Tun da farko dai Sanata Abdulaziz Yar’adua, dan marigayiyar, yay mahaifiyarsa ya yabawa gwamnati domin karramawa.
Yace "mahaifiyarmu ta kasance misali mai haske na alheri da tausayi.
“Rayuwarta shaida ce ga kimar aiki tukuru, sadaukarwa da hidima ga dan adam.
“A matsayinta na Musulma mai kishin addini, ta yi rayuwa ta bangaskiya,
a koda yaushe tana neman yardar Allah.
"Rasuwarta ta bar wani gibi da ba za a taba cikawa ba, amma muna samun
ta'aziyya da sanin cewa ta yi rayuwa mai gamsarwa kuma ta bar gadon
soyayya, alheri da karamci.(NAN)(www.nannews.ng)
SSI/ETS
Ephraims Sheyin ne ya gyara