Rikicin Boko Haram ba rikicin addini ba ne  – Zulum

Rikicin Boko Haram ba rikicin addini ba ne  – Zulum

Spread the love

Rikicin Boko Haram ba rikicin addini ba ne  – Zulum

Imani

Abdullahi Mohammed

Maiduguri, Dec. 2, 2025(NAN) Gov. Babagana Zulum na Borno ya ce rikicin Boko Haram ba rikicin addini ba ne kamar yadda wasu kungiyoyi ke nunawa.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga shugabannin addinin Musulunci da Kirista na jihar, inda ya bukaci a yi sulhu da zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar.

“Rikicin Boko Haram ba rikicin addini ba ne, cin zarafi ne ga wayewarmu, bil’adama, da duk wani abu da muke rike da shi ba tare da la’akari da akida ba.

“Yana da matukar muhimmanci mu hada kai mu kawar da duk wani labarin karya da ke neman nuna matsalar tsaronmu da launin addini, rikicin addini bare ne a gare mu.

“Masu ta’addanci sun kashe, sun raunata, tare da raba musulma da kiristoci, sun lalata Masallatai da Coci ba tare da wani hukunci ba.”

A cewar gwamnan, kididdigar da aka yi wa ‘yan da abin ya shafa na da matukar tayar da hankali.

“Yayin da duk wani rai da aka rasa abu ne na yin mai nadama, bayanai sun nuna a fili cewa mafi yawan wadanda aka kashe, aka yi garkuwa da su, da kuma gudun hijira ‘yan uwanmu Musulmai ne.

Ya ce ya kamata wannan bala’i ya dunkulr al’ummar Borno cikin bakin ciki da hadin kai domin daukar mataki daya.

Zulum ya ce shirye-shiryen gwamnatinsa na sake ginawa, sake tsugunar da su da kuma gyara suna bin ka’idojin adalci, daidaito da kuma hada kai.

“Muna sake ginawa bisa la’akari da bukatu da kuma kudurinmu na maido da zamantakewar kowace al’umma,” in ji gwamnan.

Ya ce gwamnatinsa ta sake gina cibiyoyin ibadar Kirista 45 da aka lalata a lokacin rikicin Boko Haram.

“Wannan adadin ya hada da 16 daga Hawul, 11 daga Gwoza, 10 daga Askira-Uba da 8 daga Chibok.

“Ba don wata alfarma muka yi ba, mun yi ne a matsayin wajibi, kamar yadda muka sake gina masallatai da kasuwanni da makarantu da gidaje marasa adadi.

Ya bukaci malaman addini da su ci gaba da jan hankalin mabiya addinai, tare da yin tir da tashin hankali da samar da sulhu a jihar.

Ya bayyana cewa makasudin kiran su shi ne don ya magance wani muhimmin ginshiki da zai samar da makomar zaman lafiya tsakanin al’ummar Musulmi da Kirista a jihar.

Zulum ya kuma bukaci kasashen duniya da su hada kai da jihar wajen magance musabbabin tashe-tashen hankula da ya ce bai takaita ga talauci da jahilci da yunwa da dai sauransu ba.

Da yake mayar da martani, shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Bishop John Bakeni, da takwaransa na kungiyar Jama atu Nasril Islam (JNI), Sheikh Jafar Ngamdu, sun yi alkawarin mika sakon zaman lafiya ga jama’a.(NAN) www.nannews.ng.ng.com
AOM/ YMU
Edited by Yakubu Uba
====


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *