Najeriya na asarar dala biliyan 10 a duk shekara sakamakon asarar bayan girbi – Kyari
Bayan girbi
Daga Aisha Ahmed
07030065142
Kangire, (Jigawa), Satumba 16, 2025 (NAN) Ministan Noma da Samar da Abinci, Sen. Abubakar Kyari, ya ce Najeriya na asarar dala biliyan 10 a duk shekara sakamakon asarar da ake yi bayan girbi.
Kyari ya bayyana haka ne a yayin bikin kaddamar da kungiyar noma da samar da ababen more rayuwa a karkara (GRAIN) Pulse Center a kauyen Kangire, na karamar hukumar Birnin-Kudu, Jigawa.
Ya ce ana tafka asara ne sakamakon rashin wajen ajiya, rashin ababen more rayuwa, karancin kayan sarrafawa, dumamar yanayi, ambaliyar ruwa, gurbacewar kasa, da karuwar ruwan sama a fadin kasar.
A cewarsa, noma na bayar da kusan kashi 24 cikin 100 na GDPn Najeriya, inda kananan manoma ke noma kusan kashi 70 cikin 100 na abincin kasar.
“Ta hanyar karfafa wa kananan manoma da kayan aiki na zamani, fasaha, da kasuwanni, za mu iya zakulo cikakkiyar arzikin ƙasarmu da mutanenmu,” in ji Ministan.
Kyari ya jaddada kudirin gwamnatin shugaba Bola Tinubu, na baiwa harkar noma fifiko a matsayin ginshikin kawo sauyi ga al’ummar kasar, yana mai jaddada cewa an mayar da hangen nesa zuwa aikace.
Ya bayyana yadda tsare-tsaren kamfanoni masu zaman kansu ke da muhimmancin gaske wajen karfafa tsarin abinci a Najeriya da kuma karfafa juriya kan asarar da ake yi bayan girbi.
Ministan ya ce, cibiyar pulse zata yi aiki ne a matsayin hadaddiyar cibiyar noma, samar da ababen more rayuwa, da raya karkara, ta yadda za ta hada dukkan sassan aikin gona waje guda.
Ya kara da cewa, cibiyar da aka tanadar na da kayan aiki na zamani, za ta samar da yanayi mai aminci na fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare, kuma za a yi irin ta a fadin kasar baki daya.
Har ila yau, Ministan Harkokin Waje, Amb. Yusuf Tuggar, ya jaddada karfin hadin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, wajen ci gaba.
Ya kuma yaba da yadda aka samar da irin wadannan cibiyoyi a cikin al’ummomin noma na Jigawa.
“Wannan yunkuri zai amfanar da Najeriya saboda fa’idodi da yawa, musamman haɗa kayan aiki da fasaha na zamani,” in ji Tuggar.
Ya yabawa shugaba Tinubu da gwamnan Jigawa ta Umar Namadi, kan yadda suka ba da fifiko wajen samar da abinci a cikin manufofin ci gaban su.
Gwamna Namadi ya bayyana jin dadinsa da yadda Jigawa ta karbi bakuncin cibiyar na farko a kasar, inda ya bayyana ta a matsayin wata kyakkyawar fasaha domin dorewar rayuwar karkara.
Ya ce aikin zai zaburar da tattalin arziki, tare da nuna sauye-sauyen da al’umma za su samu ta hanyar bunkasa noma.
Namadi ya bayyana cewa, wurin ya hada da tsarin hadaka mai amfani da hasken rana, cibiyoyin sadarwa na zamani, da kuma hidimomin da suka kunshi dukkan sassan darajar aikin gona.
Ya nanata kudirin gwamnatinsa na karfafa aikin gona domin samar da ayyukan yi, fadada ababen more rayuwa, da inganta rayuwa.
Shugaban Karamar Hukumar Birnin-Kudu, Mista Muhammad Uba, ya yi alkawarin ba da goyon baya ga ajandar Shugaba Tinubu, inda ya bayyana yadda jihar Jigawa ta ba da fifiko a fannin noma da samar da abinci.
Ya kara da cewa Gwamna Namadi ya dauki muhimman matakai domin kawo sauyi da kuma daidaita harkar noma a jihar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Kyari ya kaddamar da cibiyar GRAIN Pulse Centre a Kangire, a wani bangare na shirin sabunta bege. (NAN) (www.nannews.ng)
AAA/KTO
======
Fassarar Aisha Ahmed