Mutum 5 sun gurfanar a kotu kan zargin satar shanun N5.6m

Mutum 5 sun gurfanar a kotu kan zargin satar shanun N5.6m

Spread the love

Mutum 5 sun gurfanar a kotu kan zargin satar shanun N5.6m

Sata

By Joy Akinsanya

Abeokuta, Afrilu, 11, 2025 (NAN) An gurfanar da wasu mutane biyar da a ke zargi da satar shanu da kudinsu ya kai Naira miliyan biyar da dubu dari shida  ranar Juma’a a gaban kotun majistare ta Abeokuta, da ke zaune a Isabo.

Wadanda ake tuhumar: Usman Mohammed, 29, Musa Oseni, 37, Adesina Ogunwale, 60, Toyin Alayande, 42, Tobi Mudasiru, 42, wadanda ba su da wani takamaiman adireshin suna fuskantar tuhume-tuhume takwas da suka hada da hada baki, sata da karbar shanun sata.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, wadanda ake tuhumar sun ki amsa dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masu.

A cewar mai gabatar da kara, Insp. Kehinde Fawunmi, wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a wani lokaci a watan Oktoban 2024, a unguwar Ile-Ise Awo a Abeokuta da tsakar dare.

Fawunmi ya ce wadanda ake tuhumar sun hada baki ne a tsakaninsu domin sace shanu hudu na Isiaka Mumuni, Adamu Mohammed da Mohammed Sanni.

A cewar mai gabatar da kara, Usman, Oseni da Alayande sun hada baki a tsakaninsu domin sace shanu biyu da darajarsu ta kai Naira miliyan 1.8 mallakin Mumuni.

“Sun kuma sace wasu shanu biyu da kudinsu ya kai Naira miliyan biyu da dubu dari uku mallakin Mohammed da kuma saniya daya mai darajar Naira miliyan daya da rabi mallakar Sanni.

“Masu korafin sun lura da shanunsu na bacewa a hankali a duk lokacin da suka isa matsugunin su.

“Daya daga cikin dan’uwan wanda ya shigar da karar ya kama Usman da Oseni a lokacin da suke kokarin kwance igiyar saniya domin su sace ta, wanda ya kai ga kama wadanda ake kara na daya da na biyu,” in ji mai gabatar da kara.

Fawunmi ya ci gaba da cewa, binciken da aka gudanar ya kai ga kama Ogunwale da Mudasiru, dukkansu mahauta, wadanda suke karbar shanun da aka sace daga Alayande.

Lauyan mai gabatar da kara ya bayyana cewa direban mai suna Alayande ne ya kai shanun da aka sace ga mahauta da sauran masu sha’awar saye.

Fawunmi ya ce laifukan sun ci karo da sashe na 516, 383 da 390 (3) (4a) (4g) (9) na dokokin jihar Ogun na shekarar 2006.

Alkalin kotun, Mrs Olubanke Odumosu-Akeba, ta bayar da belin Usman, Oseni da Alayande a kan kudi Naira miliyan daya kowannen su tare da mutum biyu da za su tsaya masa.

Ta kuma bayar da belin Ogunwale da Mudasiru a kan kudi Naira 500,000 kowannen su tare da masu tsaya masa guda biyu kowanne a daidai adadin.

Sai dai alkalin kotun ya bayar da umarnin a tsare Usman, Oseni da Alayande a gidan gyaran hali na Ibara har sai an kammala belinsu.

Odumosu-Akeba ya dage ci gaba da sauraren karar har sai ranar 8 ga watan Mayu.(NAN)

IOJ/AOS

==========

Bayo Sekoni ne ya gyara shi


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *