Hukuma ta musanta rahoton daukar ma’aikatan shige da fice
Hukuma ta musanta rahoton daukar ma’aikatan shige da fice
Daukar Ma’aikata
Daga Yahaya Isah
Abuja, 31 ga Agusta, 2024 (NAN) Hukumar kula tare da kare hakkokin ma’aikatan gidan Gyaran Hali, Kashe Gobara, ‘Yansandan Farin Kaya da Jami’an Shige da Fice ta Kasa (CDCFIB), ta musanta shelar daukar jami’an Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) da wata kafa ta yada a yanar gizo.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren hukumar, Mista Ja’afaru Ahmed, ya fitar ranar Asabar a Abuja.
“Hukumar tana so ta sanar da jama’a cewa buga labaran da a ke yadawa ta yanar gizo ba su fito daga hukumar ba don haka ya kamata a yi watsi da su.
“Har ila yau, tana fatan gargadin jama’a da su yi taka-tsan-tsan da ayyukan kungiyoyin daukar ma’aikata na jabu da masu satar mutane,” in ji ta.
Hukumar duk da haka, ta ce daukar ma’aikata cikin Hukumar kashe gobara ta Tarayya (FFS)), a halin yanzu tana ci gaba kuma za a sanar da masu nema da a ka zaɓa tare da sanar da mataki na gaba.
Hukumar ta kara da cewa, za a yi hakan ne ta hanyar sakonnin tarho da masu asusun yanar gizo da aka bayar a lokacin da ake yin rajistar.(NAN)(www.nannews.ng)
YI/SH
====
edita Sadiya Hamza