Gwamnatin Kano ta kaddamar da ciyar da mutane 91,000 kullum ciki  watan Ramadan

Gwamnatin Kano ta kaddamar da ciyar da mutane 91,000 kullum ciki  watan Ramadan

Spread the love

Gwamnatin Kano ta kaddamar da ciyar da mutane 91,000 kullum ciki  watan Ramadan
Ciyarwa
Daga Muhammad Nur Tijjani
Kano, Maris 3, 2025 (NAN) Gwamnatin jihar Kano ta shirya ciyar da mutane 91,000 a cibiyoyi 91 da aka ware a cikin shirin ciyarwa a watan Ramadan na shekarar 2025.
Da yake kaddamar da shirin ciyarwar a karamar hukumar m Fagge da yammacin ranar Lahadi, mataimakin gwamna kuma shugaban shirin, Alhaji Aminu Abdulsalam, ya bayyana cewa shirin zai dauki tsawon kwanaki 27.

Ya ce shirin an yi shi ne da nufin tallafa wa marasa galihu da kuma samar da abincin buda baki a kullum ga musulmi masu azumi, tare da rage matsalolin da ake fuskanta a watan Ramadan.

“Tun lokacin da Gwamna Abba Kabir-Yusuf ya hau kan karagar mulki, ya kafa wannan shiri domin tallafa wa marasa galihu ta hanyar samar da abincin buda baki a kullum a cikin watan Ramadan.

“Shirin wanda wani bangare ne na ayyukan jin kai da jihar ke yi a duk shekara, yana da nufin rage wahalhalun da musulmi masu azumi ke fuskanta a lokacin azumin Ramadan.

“Gwamnatin jihar Kano ta amince da bukatar dimbin al’ummar jihar na cikin watan Azumin Ramadana, ya kuma jajirce wajen ganin an kai dauki ga mabukata,” inji shi.

Abdulsalam ya nuna jin dadinsa da yadda aka fara shirin ba tare da wata matsala ba.

Daga nan ya bukaci kamfanonin da abin ya shafa da su tabbatar da kai kayan abinci cikin gaggawa da kuma inganci ga dukkan cibiyoyin ciyar da abinci, domin cimma manufofin shirin.

Abdulsalam ya samu rakiyar manyan jami’ai da suka hada da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida Ibrahim Waiya da kuma takwaransa na ma’aikatar harkokin addini Sheikh Tijjani Auwal. (NAN) ( www.nannews.ng)

MNT/AOS

========

Bayo Sekoni ne ya gyara shi

 


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *