Gwamnatin Jihar Sokoto ta kaddamar sayar da kayan abunci N1bn ga masu karamin karfi
Gwamnatin Jihar Sokoto ta kaddamar sayar da kayan abunci N1bn ga masu karamin karfi
Kayan abinci
Daga Habibu Harisu
Sokoto, Feb. 18, 2025 (NAN) Gwamnatin jihar Sokoto ta kaddamar da shirin tallafin kayan abinci cikin rahusa na Naira biliyan daya da nufin samar da kayayyaki masu sauki ga ma’aikatan gwamnati da masu karamin karfi a kananan hukumomi shida dake fadin jihar.
Da yake jawabi a taron horar da masu gudanar da shaguna a ranar Litinin, kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Alhaji Ibrahim Dadi-Adare, ya jaddada cewa an tsara shirin ne domin inganta jin dadin ma’aikata.
Dadi-Adare ya bukaci masu gudanarwa da su kiyaye gaskiya tare da bin ka’idojin da aka kafa don tallafawa nasarar dorewar shirin.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin a karkashin Gwamna Ahmad Aliyu ta ba da jari sosai a fannin samar da ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, noma, da samar da ruwan sha, tare da magance matsalolin tsaro.
Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnati ta bullo da wasu matakai na taimakawa wadanda suka hada da tallafin sayar da shinkafa, rarraba kayan amfanin gona kyauta, da kuma zuba jari mai tsoka a fannin tsaro.
A nasa jawabin shugaban kwamatin, Alhaji Chiso Dattijo, ya bayyana cewa matakin gwaji na shirin ya shafi ma’aikatan jiha da na kananan hukumomi da kuma malaman firamare.
Ya ce kananan hukumomi shida da aka zabo na shirin farko sun hada da Dange Shuni, Wamakko, Bodinga, Kware, Sakkwato ta Arewa, da Sakkwato ta Kudu, tare da shirin fadada wasu yankunan.
Dattijo ya bayyana cewa kowane ma’aikaci zai samu damar siyan kayayyaki da darajarsu ta kai kashi 30 cikin 100 na albashin su na wata, tare da kayyade Naira 15,000 nan da makonni masu zuwa.
Ya ce an dauki wani mai ba da shawara don gudanar da hanyoyin sadarwa ta yanar gizo, gudanar da bayar da katin kiredit, aiwatar da biyan kudi, da yin rajistar biometric.
Ya kuma kara da cewa, shagunan a cike suke kuma nan ba da dadewa ba za a samu kayayyakin da za a saya.
“Masu rajista ne kawai za a ba su izinin siyan kayan, kuma za a cire su kai tsaye daga albashin ma’aikata ta hanyar ma’aikatar kudi.”
Dattijo ya bukaci ma’aikata da su baiwa manajoji hadin kai, su ziyarci shagunan da kan su, sannan su kai rahoton duk wani sabani da aka samu ga kwamitin. (NAN) (www.nannews.ng)
HMH/AMM
========
Abiemwense Moru ne ya gyara