Gwamnatin Jihar Yobe ta sanarda yiwuwar sabuwar ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 9
Gwamnatin Jihar Yobe ta sanarda yiwuwar sabuwar ambaliya ruwa a kananan hukumomi tara
Ambaliya
Daga Nabilu Balarabe
Damaturu, 11 ga Satumba, 2024 (NAN) Gwamnatin Jihar Yobe ta ce akwai yiwuwar samun sabuwar ambaliyar ruwa a kananan hukumomi tara na jihar a sakamakon shirin sakin ruwa daga madatsun ruwa na Dadinkowa da Lagdo.
Kananan hukumomin sun hada da Nguru, Bade, Karasuwa, Jakusko, Yusufari, Geidam, Tarmuwa, Bursari, Machina, Gujba da Fune.
Dokta Mohammed Goje, Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) ne ya yi wannan gargadin a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu ranar Talata.
Ya kara da cewa sakin ruwa daga madatsun ruwan guda biyu zai kara jefa mazauna yankunan cikin mawuyacin hali.
” Mazaunan wadannan garuruwan sun sha wahala sosai saboda ambaliyar da ta auku a yankin a baya, sakamakon mamakon ruwan da aka kwashe kwanaki ana yi.
“Yobe ta fuskanci ambaliyar ruwa tsakanin 15 ga Afrilu zuwa 9 ga Satumba 2024, wanda ya haifar da barna a kananan hukumomi da dama.
“Wannan shawara ta kasance gargadi saboda yiwuwar fitowar ruwa daga dam ɗin Dadinkowa, Kogin Hadeja-Jama’are, Kogin Kamodugu, da kuma dam ɗin Lagdo a Kamaru,” in ji Goje.
Sakataren zartaswar ya shawarci mazauna yankunan da su dauki matakan kariya da suka hada da kauracewa zuwa wurin da babu alamun ambaliya domin ceton rayuka da dukiyoyin su.
“Ku kasance kuna da masaniya ta hanyar sauraron bayanai akai-akai daga shugabannin alumma, kananan hukumomi da hukumar ba da agajin gaggawa ta jiha.
“Ku ci gaba da tuntuɓar gaggawa wurin hukumomi don shirin kota-kwana,” in ji shi.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa sama da gidaje 19,000 a cikin al’ummomi 432 ne ya zuwa yanzu ambaliyar ruwa ta shafa a jihar. (NAN) (www.nannews.ng)
NB/KLM
======
Muhammad Lawal ne ya gyara
NiMet ta yi hasashen samun tsawa da ruwan sama na kwanaki 3 a Najeriya
NiMet ta yi hasashen samun tsawa da ruwan sama na kwanaki 3 a Najeriya
Yanayi
By Gabriel Agbeja
Abuja, Satumba 11, 2024 (NAN) Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen samun tsawa mai karfi da ruwan sama daga ranar Laraba zuwa Juma’a a fadin Najeriya.
Wannan na cikin wata sanarwa ta yanayi da hukumar ta fitar ranar Talata a Abuja.
Hukumar ta yi hasashen tsawa a sassan jihohin Borno, Adamawa, Taraba, Yobe, Katsina, Sokoto da Kaduna da safiyar ranar Laraba a yankin arewa.
A cewar NiMet, ana sa ran tsawa a sassan jihohin Kano, Borno, Katsina, Adamawa, Kaduna, Taraba, Zamfara, Kebbi da Jigawa a cikin sa’o’i da rana.
“A yankin Arewa ta tsakiya ana hasashen tsawa a sassan babban birnin tarayya, jihohin Nasarawa da Neja da safe.
“A washegari, ana sa ran za a yi tsawa a sassan babban birnin tarayya, Nasarawa, Benue, Kogi, Neja da Kwara.
“A yankin kudu ana sa ran tsawa a sassan jihohin Oyo, Osun, Ekiti, Ogun, Ondo, Legas, Edo, Delta, Cross River da Akwa Ibom a cikin safiya,” in ji ta.
Ta yi hasashen za a samu ruwan sama na tsaka-tsaki a wasu sassan
jihohin Enugu, Ebonyi, Abia, Anambra, Edo, Ekiti, Oyo, Rivers, Cross River, Delta da Akwa Ibom.
A cewar NiMet, ana sa ran za a yi tsawa a wasu sassan jihohin Taraba da Adamawa da safe a yankin Arewa cin kasar.
An yi hasashen za a yi tsawa a sassan jihohin Kano, Kaduna, Bauchi, Jigawa, Katsina, Kebbi, Adamawa da Taraba da yammacin ranar.
“A yankin Arewa ta tsakiya, ana sa ran samun ruwan sama a wasu sassan Jihohin Filato da Binuwai da safe.
“Da rana da yamma, ana hasashen tsawa msai karfi a sassan babban birnin tarayya, Nasarawa, Kogi, Neja, Kwara da jihar Benue.
“A cikin garuruwan kudanci kuwa, ana sa ran samun ruwan sama na tsaka-tsaki a sassan jihohin Enugu da Anambra da safe,” in ji ta.
Hukumar NiMet ta yi hasashen za a samu ruwan sama a wasu sassa na
Ondo, Edo, Oyo, Osun, Ekiti, Imo, Enugu, Ebonyi, Abia, Cross River, Bayelsa, Ribas da Delta Jihohin.
Hukumar ta yi hasashen cewa za a yi tsawa a sassan jihohin Adamawa da Taraba da ke arewacin kasar a safiyar Juma’a.
Ta yi hasashen tsawa a sassan jihohin Taraba, Borno, Gombe, Bauchi, Adamawa, Kaduna, Kano, Katsina da Zamfara da yammacin ranar.
A cewar NiMet, ana sa ran samun ruwan sama a sassan Nasarawa da Neja da safe a yankin Arewa ta tsakiya.
“A washegari, ana sa ran za a yi tsawa a wasu sassa na Kogi, Babban Birnin Tarayya, Kwara da Jihar Neja.
“A cikin biranen kudanci, ana sa ran yin gajimare a safiya. Daga baya kuma, ana sa ran za a yi tsawa tare da tsammanin za a yi ruwan sama na mai sauki a kan garuruwan gabar teku,” in ji ta.
Ta bukaci mazauna yankin da su guji wuraren da ambaliyar ruwa ta fi kamari, domin akwai yiwuwar ambaliya a birane a manyan biranen saboda mamakon ruwan sama.
A cewar NiMet, iska mai karfi na iya tunkarar ruwan sama a wuraren da ake iya samun tsawa, ya kamata jama’a su yi taka tsantsan tare da bin shawarwarin tsaro da hukumomin da abin ya shafa suka bayar.
‘An shawarci jama’a da su kasance a fadake ta hanyar sabunta yanayi daga NiMet. A kuma ziyarci kundin yanar gizon mu www.nimet.gov.ng
“An shawarci ma’aikatan jirgin sama da su sami takamaiman rahotannin yanayi na filin jirgin sama (takardun jirgin sama) daga NiMet don ingantaccen shiri a cikin ayyukansu,” in ji shi. (NAN)(www.nannews.ng)
FGA/OJI/IKU
Edited by Maureen Ojinaka/Tayo Ikujuni
Ambaliyar Ruwan Maiduguri: NEDC na tantance yawan barna
Ambaliyar Ruwan Maiduguri: NEDC na tantance yawan barna


Tinubu na kokarin magance matsalolin tattalin arziki tare da tsari mai dorewa – APC
Tinubu na kokarin magance matsalolin tattalin arziki tare da tsari mai dorewa – APC
Ambaliyar ruwa: Shettima ya ziyarci Maiduguri, ya ba da tirela 50 na shinkafa
Ambaliyar ruwa: Shettima ya ziyarci Maiduguri, ya ba da tirela 50 na shinkafa
Shettima
By Yakubu Uba
Maiduguri, Satumba 10, 2024 (NAN) Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ziyarci Maiduguri a ranar Talata domin jajanta wa al’ummar Borno kan bala’in ambaliyar ruwa ta Alau da ta raba dubban mutane da gidajensu.
Kashim, wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa birnin da ke fama da rikici, ya samu tarba daga Gwamna Babagana Zulum, inda ya kai shi fadar Shehun Borno, Alhaji Abubakar El-Kanemi, wanda shi ma ambaliyar ruwa ta afkawa.
Daga fadar, mataimakin shugaban kasar ya tuka mota zuwa sansanin Bakassi inda dubban mutanen da ambaliyar ta raba da muhallansu ke samun mafaka.
Shettima ya shaida wa wadanda abin ya rutsa da su cewa gwamnati za ta tallafa musu da tirela 50 na shinkafa.
Ya kara da cewa gwamnati za ta kuma hada kai da hukumar raya yankin arewa maso gabas da sauran hukumomi don ganin ba su shafe sama da makonni biyu a sansanin ba.
NAN ta ruwaito cewa a ranar Talata mazauna Maiduguri sun farka da mummunar ambaliyar ruwa da ta lakume gine-gine da dama tare da kwashe tituna da gadoji.(NAN)
YMU/ETS
=======
Kunar Bakin wake: Masu ruwa da tsaki sun bukaci a inganta ayyukan kula da lafiyar kwakwalwa
Kunar Bakin wake: Masu ruwa da tsaki sun bukaci a inganta ayyukan kula da lafiyar kwakwalwa
Kunar Bakin wake:
Daga Abujah Racheal
Abuja, Satumba 10, 2024 (NAN) Masu fafutukar kula da lafiyar kwakwalwa sun yi kira da a inganta ayyukan kiwon lafiya, wayar da kan jama’a
da kuma bayar da tallafi don magance matsalar Kunar Bakin wake a kasa.
Sun yi wannan kiran ne a wata tattaunawa daban-daban da suka yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Talata a Abuja domin tunawa da
ranar kunar Bakin wake ta duniya ta 2024 (WSPD).
Ranar 10 ga watan Satumba a kowace shekara a fadin duniya tun daga 2003, a na wayar da kan jama’a game da halayen mutane masu kashe kansu, karin sadaukarwa da kuma nuna bukatar magance matsalolin lafiyar kwakwalwa da kuma rage kyama.
Taken wannan shekara na 2024-2026 shi ne “Canza Labarun Kunar Bakin wake, ” ya mayar da hankali kan “Gane Labarunmu” don haɓakar wayar da kai da bada tallafi.
Mista Ameh Zion, wanda ya kafa wata kungiya mai suna Mandate Health Empowerment Initiative (MHEI), ya ce taken yana nuna muhimmancin
sauya tunanin al’umma game da kunar Bakin wake, boyewa da kyama da bude kofofin bada tallafi.
Ya ce “yana ƙarfafa al’ummomi don tattauna lafiyar kwakwalwa da kunar Bakin wake, da haɓaka yanayin da mutane ke jin daɗin neman taimako
ba tare da tsoron hukunci ba.”
Zion ya yi nuni da cewa, a Najeriya, kyamar da ke tattare da matsalar tabin hankali kan hana mutane neman taimako, lamarin da ke kara ta’azzara matsalar.
Ya bukaci gwamnati da ta samar da tsare-tsare da za su karfafa tattaunawa kan rigakafin kunar bakin wake, yana mai jaddada cewa “kowane zance, komai
kankantarsa, yana ba da gudummawa wajen karya shinge da wayar da kan jama’a.”
Hon. Mohammed Usman, wanda shi ne wanda ya kafa kungiyar Lafiya Wealth Initiative, ya yi wannan kiran a kan samun karin tattaunawa a fili domin rage kyama da kuma daidaita neman taimako.
Usman ya bayyana bukatar shigar da rigakafin kunar bakin wake cikin bada shawara tare da yin kira ga gwamnatocin jihohi da na tarayya da su ba da fifiko ga
hanyoyin kula da lafiyar kwakwalwa da tsarin tallafi.
Ya ce akwai karancin kwararrun likitoci a kasar nan, musamman a fannin tabin hankalin da lafiyar kwakwalwa inda ya kara da cewa “ duk da yawan al’ummarta fiye da miliyan 200, Najeriya na da likitan kwakwalwa daya kacal ga kowane mutum miliyan daya.
“Wannan babban gibi ne a cikin samun kulawar lafiyar kwakwalwa.”
Ya kuma yi nuni da cewa, yawancin likitocin masu fama da tabin hankali sun taru ne a birane da yankunan kudancin kasar, wanda hakan ya sa wasu yankunan ba su da wani aiki sosai.
Dokta Ifeoma Nwachukwu, kwararriyar lafiyar tabin hankali, ta jaddada mahimmancin samar da yanayi mai taimako ga lafiyar kwakwalwa.
Ta ce “Tabin hankali yana da mahimmanci kamar lafiyar jiki. Muna bukatar mu karya shirun game da tabin hankali tare da samar da wadatattun albarkatu. “
Nwachukwu ya soki tsarin biyan kuɗi daga aljihu don kula da lafiyar kwakwalwa, tare da lura da cewa matsalolin tattalin arziƙi na iya hana mutane samun magungunan da suka dace, wanda ke iya dagula yanayin su.
Ta kuma yi gargadin cewa matsalolin tattalin arziki na iya haifar da dagulewar lamuran lafiyar kwakwalwa, har ma wadanda ba su da wani yanayi na iya fuskantar tunanin kashe kai
a sakamakon.
Ta shawarci ‘yan Najeriya da ke fuskantar irin wannan damuwa da su nemi taimakon kwararru, maimakon shan wahala cikin shiru ko kuma dogaro da cibiyoyin addini.
A halin da ake ciki, Ms Funke Akin, wata malamar da ta rasa wani masoyinta har ta kashe kanta, ta ce ta zama mai ba da shawara kan lafiyar kwakwalwa.
Ta ce “mummunan rashi na ɗan’uwana ya sa na ba da shawara don ingantacciyar kula da lafiyar kwakwalwa da tallafi.”
NAN ta tuna cewa rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya na 2020 ya nuna cewa kusan kashi 30 cikin 100 na ‘yan Najeriya na da wasu nau’in tabin hankali.
Abubuwa kamar cutar ta COVID-19, batutuwan tsaro, rashin aikin yi, da ƙalubalen tattalin arziƙi sun iya dagula kididdigar. (NAN) (www.nannews.ng).
AIR/HA
Garin Maiduguri ya cika da ruwa yayin da madatsar ruwan Alau ta datse
Garin Maiduguri ya cika da ruwa yayin da madatsar ruwan Alau ta datse
Ambaliyar ruwa
By Yakubu Uba
Maiduguri, Satumba 10, 2024 (NAN) Mazauna Maiduguri a Borno sun kasance cikin shirin ko-ta-kwana yayin da ambaliyar ruwa ta mamaye gidaje da dama biyo bayan rushewar madatsar ruwa ta Alau da ta cika mako guda da ya gabata.
A wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Tsaro na Cikin Gida, Farfesa Usman Tar, ya fitar a safiyar ranar Talata mai taken “Flooding Alert for Residents Bank of River” ta bukaci a kwashe mutanen da abun zai shafa cikin gaggawa.
Ya ce, “Saboda yawan ruwan da ba a saba gani ba a bana, muna kira ga daukacin mazauna bakin kogi da su dauki matakin kare kansu da dukiyoyinsu cikin gaggawa.
“Ruwan Alau Dam ya fasa wata tashar da a yanzu haka ke lalata gonaki kuma ruwan ya nufi gabar kogi.”
Tar ya kuma bukaci mazauna yankunan da abin ya shafa da su bi hanyoyin ficewa domin tabbatar da tseratar da lafiyarsu.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, a karo na karshe da madatsar ruwan ta samu irin wannan matsala shi ne a shekarar 1994, wanda hakan ya haifar da ambaliya da ba a taba ganin irinta ba a Maiduguri inda kusan rabin garin ya cika. (NAN) (www.nannews.ng)
YMU/BRM
==========
Edited by Bashir Rabe Mani
Masani ya ba gwamnatoci shawarar tabbatar da zaman lafiya a cibiyoyin karatu
Masani ya ba gwamnatoci shawarar tabbatar da zaman lafiya a cibiyoyin karatu
Safety
Daga Fatima Mohammed-Lawal
Ilorin, Satumba 9, 2024 (NAN) Wani Farfesa a Sashen Kere-Kere na Jami’ar Ilori, John Olorunmaiye, ya bukaci gwamnatoci su dau dukkan matakai don tabbatar da tsaro a cibiyoyin karatu fake fadin kasa.
Olorunmaiye, ya bada shawarar ne yayin da yake magana a taron shekara-shekara karo na 11 (AGM) na kungiyar injiniyoyi ta Najeriya reshen jihar Kwara a Ilorin, ya ce hakan zai taimaka wajen karfafa ilimi mai inganci.
Ya bayyana cewa sai a lokacin da cibiyoyin suka samu cikakkiyar kulawa za su samu karfafawa da ba dalibai natsuwa da maida hankali wajen koyon karatu.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa taken taron shi ne “Ilmi da sakamako mai kyau ta hanyar Kere-Kere: Cikin Salo da tsaro mai gamsarwa”
Olorunmaiye ya lura da cewa idan aka aiwatar da ilimin da ya dogara da sakamako da kyau, kowane ɗalibi zai zama mai hazakar koyo.
Ya koka da yadda kasar nan ke fama da kalubale na rashin isassun adadi ko ingancin ma’aikatan ilimi da masu koyarwa a jami’o’i da dama.
Masanin ya bayyana cewa akwai daliban da suka yi fice a wasu jami’o’i, musamman jami’o’in gwamnati, duk da rashin kayan aiki na zamani a dakunan gwaje-gwaje.
“Akwai rashin kulawa ko watsi da dakunan gwaje-gwaje ga masu fasaha da malamai a wasu jami’o’i, marasa ƙarfi ko mara kyaun shirye-shiryen horar da masana’antu da ma’aikata marasa ƙarfi da sauransu,” in ji shi.
Olorunmaiye, wanda tsohon shugaban Injiniya da Fasaha ne, ya kuma bayyana cewa aiwatar da shirin ba da lamuni na dalibai da shugaba Bola Tinubu ya yi abin yabawa ne matuka.
Ya yi ikirarin cewa a baya-bayan nan ne asusun bayar da lamuni na ilimi na Najeriya (NELFUND) ya raba sama da Naira biliyan 1.1 na kudin karatu ga dalibai kusan 20,000 a wasu manyan makarantun gwamnati.
“Ya kamata kuma a ba da lamunin NELFUND ga ɗaliban da suka kammala karatun digiri a cikin shirye-shiryen Injiniya, saboda hakan zai ba da damar horar da ɗalibai da yawa.”
Olorunmaiye ya ci gaba da cewa, duk dalibin da ya kammala karatunsa a fannin Injiniya dole ne ya kasance yana da ikon yin amfani da ilimin Lissafi, Kimiyyar dabi’a, na’ura mai kwakwalwa da ƙwararrun Injiniya.
“Dole ne shi ko ita ya iya samar da hanyoyin magance matsalolin Injiniya masu rikitarwa,” in ji shi.
A jawabinsa, Shugaban reshen mai barin gado, Suleiman Yahaya na Sashen Injiniya na Jami’ar Ilorin, ya yabawa ‘yan kungiyar bisa goyon bayan da suka bayar.
Ya tuna cewa aikin shugabancin Reshen bai kasance mai sauƙi ba domin ya ƙunshi sadaukarwa sosai.
Yahaya ya ce tallafin da aka samu ya haifar da gagarumar nasara, wadanda suka hada da inganta da inganta hadin gwiwa da cibiyoyi daban-daban da dai sauransu.
“Ina kira ga kowa da kowa ya marawa sabuwar gwamnati baya domin samun karin sakamako mai kyau,” in ji shi.(NAN)(www.nannews.ng)
FATY/OLAL
=========
(Edited by Olawale Alabi
‘Yan sanda ssun cafke wani matasbi kan zargin kisan kakar sa da kawun sa
‘Yan sanda ssun cafke wani matasbi kan zargin kisan kakar sa da kawun sa
Kisa
Daga Suleiman Shehu
Ibadan, Satumba 9, 2024 (NAN) Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da tsare wani mutum mai matsakaicin shekaru dangane da zargin kisan kakansa da kawunsa a unguwar Apete da ke Ibadan.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Oyo, SP Adewale Osifeso, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani sako da ya aikewa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Ibadan ranar Litinin.
Osifeso ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike domin gano dalilin da ya sa ta aikata wannan aika-aika.
Ya kara da cewa za a ba wa jama’a bayanai bisa ga hakan.
“An fara bincike kan lamarin, yayin da za a ba da bahasin yadda ya kamata,” in ji shi.
NAN ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6.00 na yammacin ranar Lahadi.
Wanda ake tuhumar, mai suna Ahmed, yana zaune ne a gida daya tare da mahaifinsa mai nakasa da kuma kawunsa mara lafiya. (NAN) (www.nannews.ng)
SYS/KOLE/MAS
==========
Remi Koleoso da Moses Solanke ne suka gyara