NAN HAUSA

Loading

Cunkoso: Masu ruwa da tsaki sun bukaci alkalai su yi la’akari da zabin hukunci

Cunkoso: Masu ruwa da tsaki sun bukaci alkalai su yi la’akari da zabin hukunci

Cunkoso

Daga Habibu Harisu

Sokoto, Agusta 29, 2024 (NAN) Kungiyar masu ruwa da tsaki kan gyara harkokin shari’a a jihar Sokoto sun bukaci alkalai da su yi la’akari da wasu zabuka na hukunta wadanda aka yankewa hukunci ba dauri ba a kowane lokaci.

Kiran na daga cikin kudurorin da Mr Rabi’u Gandi, wakilin kungiyoyin farar hula ya karanta a karshen taron masu ruwa da tsaki a ranar Laraba a Sokoto.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa taron mai taken “Fahimtar Dabarun Tsaretsaren Tsaro na Kasa, Samar da Ingantaccen Yanayi ga Ma’aikatan gwamnati da wadanda ba na Gwamnati ba”, wata kungiya ce mai zaman kanta ta CLEEN Foundation ce ta shirya tare da tallafi daga gidauniyar MacArthur.

Ya ce bisa la’akari da shawarwarin da masu ruwa da tsaki suka bayar, akwai bukatar alkalai a kowane mataki su rika amfani da zabukan yanke hukunci kamar ayyukan al’umma da sauran hukunce-hukunce, ba zaman gidan yari ba a kodayaushe.

Ya bayyana cewa mafi yawan kashi na hukunce-hukuncen dauri sun sanya wuraren gyaran Hali cikin cunkoso, yana mai jaddada cewa yin amfani da zabin zai rage cunkoso.

Gandi ya kuma shawarci bangaren shari’a da ‘yan majalisar dokokin kasar da su saukaka tsarin sahhalewa masu laifi da sharadin kimtsuwa a mulkin kasar domin inganta tsarin.

Ya kuma kara jaddada mahimmancin tsarin sahhalewa fursunonin a Najeriya, wanda zai rage matsin lamba ga wuraren da ake tsare da su, da yawan barkewar gidan yari da korafe-korafe a tsakanin fursunonin.

A cewarsa, wakilan hukumomin tabbatar da doka a wurin taron sun ba da bayanai da shawarwari daban-daban kan mafi kyawun hanyoyin inganta ayyukansu da kuma kalubalen da suke fuskanta a kasar.

Yayin da ya yabawa gidauniyar CLEEN bisa wannan kokarin, Gandi ya ce za a tattara bayanan tare da mikawa hukumomi na gaba domin tantancewa da aiwatar da su.

Da yake jawabi, jami’in shirin na gidauniyar, Mista Ebere Mbaegbu, ya ce taron tattaunawar wani bangare ne na hadakar ‘yan kasa da masu ruwa da tsaki na gwamnati da wadanda ba na gwamnati ba a kan sauye-sauyen aikin ‘yan sanda da shari’a, gudanar da hukunce hukuncen laifuka da shari’a ta tanadar, gaskiya da rikon amana.

Mbaegbu ya bukaci aiwatar da tsarin sahhalewa fursunoni a matsayin mabudin rage cunkoso a gidajen yari da dabarun gyara masu laifi.

Ya jaddada cewa gudanar da adalci shi ne ginshikin duk wata al’umma da ta tabbatar da bin doka da oda.

Ya kara da cewa kokarin hadin gwiwa na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da cewa wannan ginshikin ya kasance mai karfi da inganci.

“ Sahhalewa fursunoni wani muhimmin bangare ne na tsarin shari’ar mu, da nufin gyara masu laifi da kuma mayar da su cikin al’umma a matsayin ‘yan kasa masu bin doka da oda.

“Yana nuna ma’auni tsakanin matakan ladabtarwa da kuma buƙatar gyarawa, sanin cewa yuwuwar yin gyare-gyare da canji mai kyau yana samuwa a cikin kowane rayuwar bil’adama,” in ji shi.

Wani bangare na mahalarta taron sun nuna godiya ga wadanda suka shirya taron, inda suka ce taron ya samar musu da wani dandali mai kima da za su iya shiga tattaunawa mai mahimmanci.

Mahalarta taron sun bayyana ra’ayoyinsu tare da tantance halin da tsarin shari’a ke ciki game da sahhalewa fursunoni da kuma babban tasirinsa kan gudanar da shari’ar laifuka a Najeriya.

NAN ta ruwaito cewa mahalarta taron sun hada da kungiyoyin fararen hula, ‘yan sanda, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), Hukumar Kula da Gyaran Hali ta Kasa (NCoS), Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), masu gabatar da kara da lauyoyi, da dai sauransu.(NAN) ( www.nannews .ng )

HMH/BRM

=========

Tace wa: Bashir Rabe Mani

Hukuma ta kori jami’ai 3, ta kuma sauke mutum 1 a matsayin albashi bisa zargin rashin da’a a Naija

Hukuma ta kori jami’ai 3, ta kuma sauke mutum 1 a matsayin albashi bisa zargin rashin da’a a Naija

 

Kora

Daga  Rita Iliya

Minna, 26 ga Agusta, 2024 (NAN) Hukumar da ke kula da harkokin shari’a a Neja ta ce ta kori wasu manyan ma’aikata uku daga aiki tare da rage ma’aikaci mai daraja biyu daraja bisa zarginsa da rashin da’a.

A wata sanarwa da sakatariyar hukumar Hajiya Hauwa Isah ta fitar a Minna ranar Litinin, ta yi zargin rashin da’a ga jami’an da abin ya shafa.

Isa ya ce ma’aikatan da abin ya shafa sun hada da Mohammed Abubakar da Ahmed Usman da Usman Isah dukkansu daga babban kotun shari’a yayin da Fatima Sambo ta rage mata matakin digiri biyu.

Ta ce korar ta biyo bayan wasu manyan ayyuka da ake zargin sun sabawa tanadi na 58 na dokokin hukumar.

Sanarwar ta ce Mohammed Abubakar mai rike da sarautar gargajiya ne na “Galadima Raba Nupe’, an same shi da laifi a karkashin doka ta 58 (1) (1) (111) da (v) saboda rashin bin umarnin halal.

Isa ya ce Abubakar ya ki ci gaba da canja sheka kuma bai yi aiki ba daga watan Nuwamba 2023, har zuwa yau ba tare da izini ko wani dalili ba.

“A cikin martanin da ya bayar game da tambayar da hukumar ta yi, ya amince da zama mataimaki na musamman ga wani basaraken gargajiya tsawon wasu shekaru yanzu,” in ji ta.

A cewarta, hukumar ta gudanar da aikinta na ladabtarwa a karkashin kundin tsarin mulkin kasar na 1999 (kamar yadda aka yi wa kwaskwarima), ta gudanar da taron gaggawa karo na 143 da ta gudanar a ranar Alhamis.

Isa ya ce, “Hukumar ta kori ma’aikata uku tare da rage ma’aikata guda daya a karkashin doka ta 72 da 73 na dokokin hukumar na shekarar 2018.

“Ma’aikatan uku da aka kora wadanda dukkansu ‘yan bangaren babban kotun ne: Mohammed Abubakar (Galadiman Raba Nupe), Ahmed Usman, da Usman Isah, yayin da Fatima Sambo ta rage mata matakin digiri biyu.

“Korar ma’aikatan ukun ya biyo bayan wasu manyan ayyuka da suka sabawa ka’ida ta 58 na dokokin hukumar.”

Ta bayyana cewa hukumar ta gano abubuwan da suka aikata a matsayin abin zargi da kuma rashin da’a.

Isa ya kara da cewa Ahmed Usman, babban magatakarda a ma’aikatar shari’a, an gurfanar da shi ne a gaban kuliya bisa aikata muguwar dabi’a da kuma almundahana.

Ta kara da cewa, an gano Usman da karkatar da kudade har sama da N600,000 da kwamitin bincike ya gudanar.

“Wannan matakin ya saba wa tanadin doka 58 (1) (III) (V) & (VI),” in ji ta.

Har ila yau, Usman Isah, babban magatakarda na II mai aiki da Kotun Majistare ta 3, Minna, an same shi da laifin rashin halartar aiki ba tare da izini ko wani dalili ba, a karkashin doka ta 58 (1) (III).

Ta ce an samu Isah ya yi watsi da aikin sa sama da watanni shida.

Haka kuma, Fatima Sambo, babbar mai rejista a sashin shari’a an same ta da laifin yin sakaci da kuma almubazzaranci da kudaden shiga da kwamitin bincike ya yi.

Isa ya ce hukumar ta yanke shawarar yin amfani da takunkumin da ya dace kan ma’aikatan da suka yi kuskure domin kare mutuncin bangaren shari’a da kuma tabbatar da amincin jama’a kan tsarin. (NAN) (www.nannews.ng)
RIS/BRM

===========

Bashir Rabe Mani ya tace

Tinubu da Abdulsalam sun kalubalanchi shashen shari’a da samar da adalchi ga kowa 

Tinubu da Abdulsalam sun kalubalanchi shashen shari’a da samar da adalchi ga kowa

Shari’a
By Taye Agbaje
Abuja, Aug.22,2024(NAN) Shugaban Kasa Bola Tinubu a ranar Alhamis yayi kira ga mambobin shashem Shari’a da su jajirce a wajen yin ayyukan su na tabbatar da adalchi ga kowa.
Tinubu yayi magana a wurin kaddamar da wani littafin tarihi kan tsohon Babban Alkalin Alkalan Najeria, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola mai ritaya.
Kamfanin Dillanchin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Mai Shari’a Kudirat Kekere-Edun ke zata maye gurbin Ariwoola a yau Juma’at.
Ariwoola yayi ritaya ne a ranar 22 ga watan Agusta bayan ya cimma shekaru 70 da haihuwa Kamar yadda dokar kasa ta samar.
Maitamakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ne ya wakilchi Tinubu a wurin taron mai cike da tarihi.
Shugaban kasar yayi kira ga maakatan shashem shari’a da kada suyi kasa guiwa domin domin tunanin wadansu yan masu ganin cewa sashen shariar bai yin aiki yadda ya kamata madamar dai baa yi masu abunda suke so ba.
Timibu ya kuma jinjina ma shashen shariar kan wadansu hukunche hukunche da suka yanke kamar irin wanda suka zartas kwanan nan kan yancin cin gashin kai na kananan hukumomin Najeriya.
Ya yaba wa Ariwoola kan chanje chanje da ya samar a sashen sharia wadanda suka kara inganta samar da adalchi ga yan kasa.
Tinubu ya kuma nuna jin dadin sa ga wannan ci gaban ya kuma yi fatar cewa wadda zata gaje shi zata dore da wadannan chanje chanjen.
Tinubu Kuma ya kara jinjina ma Ariwoola yana mai jinjina masa kan dogewar sa da zurfin tunani wanda ya kara taimakawa wurin samar da adalchi ga yan kasa.
Shi ma tsohon shugaban kasar Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, wanda shine shugaban taron, yayi kira ga Alkalai da su tabbatar da samar da adalchi ga kowa.
Yace ya kamata su yi hakan ba tare da nuna bambanchin yare, adding ko siyasa ba.
Abubakar ya kuma yaba wa Ariwoola kan dunbin nasarorin da ya samu a cikin shekarun biyu da ya jagoranchi shahen shariar kasar nan.
Ya kuma yi kira ga yan Najeriya da su kwaikwayi kyawawan halaye na Ariwoola wajen nuna gaskiya da daidaito a dukkan harkokin su.
Shima Shugaban Kotun Maikata ta Kasa watau Industrial Court, Mai Shari’a Benedict Kanyip yace littafin wani kundi tarihi ne da kowa ya kamata ya karanta.
Ita ma wadda zata gaji Ariwoola , Kekere-Ekun ta jinjina Wanda zata gadar da cewa shi gwarzo ne kuma mai dinbin kamala.
Shima babban Sarki, Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, Ojaja 11, ya ce Ariwoola ya bar misalai na kwarai da za’a yi kwaikwaya a shashen shari’ar Najeriya. ( NAN) (www.nannews.ng)
TOA/SH
===============
Edited by Sadiya Hamza
Tace wa : Bashir Rabe Mani