NAN HAUSA

Loading

Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje, gonaki 80 a Langtang ta Kudu

 

Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje, gonaki 80 a Langtang ta Kudu

Ambaliyar ruwa

By Polycarp Auta

Jos, Oktoba 6, 2024 (NAN) Wata mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a karamar hukumar Langtang ta Kudu a jihar Filato, ta lalata gidaje da gonaki 80.

Ambaliyar wadda ta afku a tsakanin Juma’a da Lahadi, ta raba dubban mutane da muhallansu tare da yin awun gaba da kayayyakinsu.

Saidai an yi sa’a, ba ta yi asarar rayuka ba.

Mista Yintim Nimilam, sakataren kungiyar ci gaban al’ummar Sabon Gida, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, inda ya bayyana yadda sama da iyalai 80 suka rasa matsugunnansu.

“Yan gudun hijirar suna neman mafaka a gurin makwabta, abokai, da dangi,” ya ce.

Wani mazaunin garin, Mista Nandul Solomon, ya bayyana damuwar al’ummar, inda ya yi kira da gwamnati da ta dauki matakin gaggawa domin rage musu radadi.

“Muna kira ga gwamnati da hukumomin da abin ya shafa da su kawo mana dauki.” (NAN) ( www.nannews.ng )

AZA/AMM

Abiemwense Moru ne ya gyara

Fassara daga Nabilu Balarabe

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

ICRC ta kwashe mutane 117 daga cibiyoyin kiwon lafiya 4 a Maiduguri

 

ICRC ta kwashe mutane 117 daga cibiyoyin kiwon lafiya 4 a Maiduguri

Ficewa

Daga Franca Ofili

Abuja, Satumba 23, 2024 (NAN) Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce ta kwashe mutane 117 daga cibiyoyin kiwon lafiya hudu da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Borno.

Aliyu Dawobe, jami’in hulda da jama’a na ICRC ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a ranar Litinin a Abuja.

Ya ce kungiyar ta kuma bayar da gudummawar jakankuna 150 ga hukumar NRCS, da asibitin kwararru na jihar da kuma hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar.

“ Madatsar ruwan Alau ta fashe ne da sanyin safiyar ranar 10 ga watan Satumba, abinda ya haddasa ambaliyar ruwa a Maiduguri.

“Kafin faruwar lamarin, ruwan sama kamar da bakin kwarya ya mamaye yankuna da dama a jihar lamarin da ya shafi hanyoyin shiga.

“Fiye da mutane 414,000 ne abin ya shafa tare da lalata gidaje da dama da amfanin gona.

“Akwai matukar damuwa ga fararan hula wadanda rikicin yankin ke cigaba da shafa,” in ji Dawobe.

A cewarsa, hadakar kungiyoyin agaji na ICRC da na NRCS ne ya shiga aikin bincike da ceton.

Ya ce sun kuma gudanar da aikin kwashe marasa lafiya tare da bayar da agajin gaggawa, da kuma hada kan iyalai da ambaliyar ruwa ta raba su da kuma kula da gawarwaki cikin aminci.

“Kungiyoyin sun kwaso gawarwaki 22 zuwa yau, yayin da yara 76 suka koma ga iyalansu.

“An kwashe mutane 117 daga cibiyoyin kiwon lafiya hudu da ruwan ya shafa.

“Hukumar ICRC ta kuma ba da gudummawar jakunkuna 150 ga NRCS, Asibitin Kwararru na Jiha da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA).

“NRCS ta kaddamar da ayyukan inganta tsafta a sansanoni uku da su ka karbi bakuncin al’ummomin da ambaliyar ruwa ta shafa tare da hadin gwiwar ICRC,” in ji Dawobe.

Dawobe ya ce a wani bangare na shirin rigakafin cutar kwalara, ICRC ta tanaji magunguna da suka hada AquaTabs da hodar chlorine don shirin ko ta kwana.

“Ana horar da masu aikin sa kai na NRCS kan yadda ake amfani da wadannan kayan kuma suna ba da fifiko wajen tsaftace rijiyoyi, famfunan hannu, rijiyoyin burtsatse, da sauran hanyoyin ruwa na al’umma.

“ICRC ta shirya zaman tallafi na zamantakewa don ma’aikatan NRCS da masu sa kai waɗanda suka shiga cikin ayyukan mayar da martani da yawa.

“A cikin kwanaki masu zuwa, ICRC tare da haɗin gwiwa tare da NRCS, za ta mika muhimman kayan gida ga gidajen da abin ya shafa, ciki har da taburmai, barguna, kayan dafa abinci, gidajen sauro, bokiti, sabulu, kayan tsaftacewa da tufafi, ” Yace.

A cewarsa, ICRC ta kuma taimaka wa Nijar, Kamaru da Chadi don magance matsalar ambaliyar ruwa.(NAN)( www.nannews.ng)

FNO/AMM

Fassara daga Nabilu Balarabe

=======

 

Gwamnatin Jihar Yobe ta sanarda yiwuwar sabuwar ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 9

 

Gwamnatin Jihar Yobe ta sanarda yiwuwar sabuwar ambaliya ruwa a kananan hukumomi tara

Ambaliya

Daga Nabilu Balarabe
Damaturu, 11 ga Satumba, 2024 (NAN) Gwamnatin Jihar Yobe ta ce akwai yiwuwar samun sabuwar ambaliyar ruwa a kananan hukumomi tara na jihar a sakamakon shirin sakin ruwa daga madatsun ruwa na Dadinkowa da Lagdo.

Kananan hukumomin sun hada da Nguru, Bade, Karasuwa, Jakusko, Yusufari, Geidam, Tarmuwa, Bursari, Machina, Gujba da Fune.

Dokta Mohammed Goje, Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) ne ya yi wannan gargadin a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu ranar Talata.

Ya kara da cewa sakin ruwa daga madatsun ruwan guda biyu zai kara jefa mazauna yankunan cikin mawuyacin hali.

” Mazaunan wadannan garuruwan sun sha wahala sosai saboda ambaliyar da ta auku a yankin a baya, sakamakon mamakon ruwan da aka kwashe kwanaki ana yi.

“Yobe ta fuskanci ambaliyar ruwa tsakanin 15 ga Afrilu zuwa 9 ga Satumba 2024, wanda ya haifar da barna a kananan hukumomi da dama.

“Wannan shawara ta kasance gargadi saboda yiwuwar fitowar ruwa daga dam ɗin Dadinkowa, Kogin Hadeja-Jama’are, Kogin Kamodugu, da kuma dam ɗin Lagdo a Kamaru,” in ji Goje.

Sakataren zartaswar ya shawarci mazauna yankunan da su dauki matakan kariya da suka hada da kauracewa zuwa wurin da babu alamun ambaliya domin ceton rayuka da dukiyoyin su.

“Ku kasance kuna da masaniya ta hanyar sauraron bayanai akai-akai daga shugabannin alumma, kananan hukumomi da hukumar ba da agajin gaggawa ta jiha.

“Ku ci gaba da tuntuɓar gaggawa wurin hukumomi don shirin kota-kwana,” in ji shi.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa sama da gidaje 19,000 a cikin al’ummomi 432 ne ya zuwa yanzu ambaliyar ruwa ta shafa a jihar. (NAN) (www.nannews.ng)
NB/KLM
======
Muhammad Lawal ne ya gyara

 

NIWA za ta kawar da jiragen ruwan katako a Kaduna

NIWA za ta kawar da jiragen ruwan katako a Kaduna

Jirgin ruwa
Daga Aisha Gambo
Kaduna, Satumba 9,2024 (NAN) Hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa (NIWA) reshen jihar Kaduna, a ranar Litinin ta bayyana cewa za ta sa a daina amfani da kwale-kwalen katako a jihar nan da shekaru biyu masu zuwa.
Manajan yankin, Isa Aliyu ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ofishin shiyyar Kaduna.
 Na biyu na hagu, Bashir Rabe-Mani, Manaja na shiyyar NAN Kaduna, Isah Aliyu, Manajan Area NIWA Kaduna.
Ya bayyana cewa hukumar tana ganawa da masu gudanar da kwale-kwale a jihar domin ganin yadda za su kafa kungiya domin saukaka fita daga cikin jiragen na katako.
“Yawancin hadurran da aka samu a magudanan ruwanmu suna tare da kwale-kwalen katako ko kwalekwale; shi ya sa za mu sauƙaƙe yadda waɗannan ma’aikatan za su iya samun jiragen ruwa masu sauri.
“A halin yanzu, muna da jiragen ruwa masu sauri guda hudu a ofishinmu da muke ba da hayar ga masu gudanar da aiki, muna shirin danganta su da kungiyoyi ko kamfanonin da za su samar da wadannan jiragen ruwa,” in ji shi.
Aliyu ya bayyana cewa NIWA tana wayar da kan jama’a a yankunan da ke kusa da kogin Kaduna kan bukatar yin amfani da rigunan ceto da kuma kauce wa cikar jiragen ruwa.
Aliyu ya ce hukumar za ta hada kai da NAN domin kara wayar da kan jama’a kan matakan tsaro da ya kamata su dauka yayin hawa cikin ruwa.
Ya bukaci masu gudanar da kwale-kwalen da su kawar da kwale-kwalen katako da suka girmi shekaru biyar sannan su rika amfani da kwale-kwalen da rana don guje wa hadurra.
Manajan yankin ya ce wadannan ka’idojin na daga cikin ‘Dokar safarar kaya ta 2023’, inda ya kara da cewa za a ci tarar wadanda suka saba wa ka’idar tarar ko kuma a kai su kotu domin gurfanar da su a gaban kuliya.
A cewarsa, fasinjoji na da alhakin barin jirgin ruwa da zarar ma’aikacin bai samar da rigunan ceto ba, kuma yana iya neman masu aikin da su daina gudu.
Ya bukaci mazauna yankin da su daina yin gini a kan “yancin hanya”, wanda ke da nisan mita 100 daga ruwan don guje wa ambaliya da lalata dukiyoyi.
Da yake mayar da martani, Manajan shiyyar, Bashir Rabe-Mani ya bada tabbacin tawagar NIWA ta NAN ta bada goyon baya wajen ganin an yada ayyuka da ayyukan hukumar ga jama’a.
Ya kara da cewa NAN ita ce kan gaba wajen samar da bayanai a kasar nan da ke zama cibiyar labarai ga dukkanin kungiyoyin yada labarai na kasar nan.
“A matsayina na Kamfanin Dillanci, NAN na da alhakin zamantakewa don fadakar da jama’a kan matakan tsaro da za su dauka yayin da suke kan hanyar wucewa domin kare rayuka da dukiyoyi.” (NAN) (www.nannews.ng)
AMG/BEN/BRM
================
 Benson Ezugwu/Bashir Rabe Mani suka tace

Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 20, ta raba 2,000 da gidajensu a Yobe

 

Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 20, ta raba 2,000 da gidajensu a Yobe

Ambaliyar
Daga Nabilu Balarabe
Gashua (Yobe), 7 ga Satumba, 2024 (NAN) Mutane 20 ne suka mutu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a karamar hukumar Bade ta jihar Yobe tun farkon watan Agusta, in ji shugabanta, Alhaji Babagana Ibrahim.

Ibrahim ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya, (NAN) ranar Juma’a a Gashua cewa yawancin wadanda suka mutun sun makale ne a karkashin baraguzan gidajen laka da suka ruguje.

Ya ce ambaliyar ta lalata gidaje sama da 10,000 kuma ta yi awun gaba da filayen noma a cikin ya Kuna kusan 200.

Shugaban ya lissafa kauyukan da bala’in ya fi shafa da suka hada da Misilli, Lawan Musa, Dagona, Dala, Katuzu da Sabongarin Gashua.

Ya ce mutane 2,000 da ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu suna samun mafaka a sansanoni uku  da a ka Taba da a Gashua.

Ya lissafa sansanonin a da suka hada da Goodluck, Zango 2 da Babuje.

Ibrahim ya ce majalisar karamar hukumar tana kokarin ciyar da ‘yan gudun hijirar abunci tun lokacin da suka zo sansanonin.

Ya ce kwanan nan Sanata Ahmed Lawan, tsohon shugaban majalisar dattawa ya bayar da gudummawar naira miliyan 10 ga wadanda abin ya shafa, yayin da gwamnatin jihar tuni ta fara raba kayan abinci ga wadanda abin ya shafa.

Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta kai dauki ga wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su wadanda a kullum yawansu ke karuwa.

“ Mutane na cikin halin kaka-ni- kayi saboda girman wannan ibtila’in da ya faru kuma ya sha karfin karamar hukumar Bade.

“Don haka ne nake kira ga gwamnatin tarayya ta hannun Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), da ta kawo mana agaji, ganin yadda ’yan gudun hijira ke ci gaba da karuwa,” in ji shi.(www.nannews.ng) (NAN)

NB/ETS

 

Hamada na tilastawa mutane tserewa daga gidajensu a Jihar Yobe – Shugaban hukuma

Tapkin Tulo Tulo dake karamar hukumar Yusufari a jihar Yobe

 

Hamada na tilastawa mutane tserewa daga gidajensu a Jihar Yobe – Shugaban hukuma

Hamada
By Nabilu Balarabe
Damaturu, Augusta 30, 2024 (NAN) Kwararowar Hamada na cigaba da tilastawa al’umomi da dama a karamar hukumar Yusufari ta jihar Yobe barin yankunansu na asali.

Shugaban karamar hukumar, Alhaji Baba Aji, ya bayyana hakan ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Damaturu ranar Juma’a.

Ya ce dunkulewar yashi ya mamaye filaye da gidaje a cikin gundumominsu, lamarin da ya hana mutane da dabbobi da yawa cigaba da zama a yankunan.

“ Hamada ta kori mutane da yawa daga asalinsu. Wasu daga cikin wadannan mutanen yanzu haka suna samun mafaka a kauyen daban daban.

“Idan ka je kauyukan da abin ya shafa za ka ga dunkulewar yashi na ci gaba da matsowa kusa da gidaje.

“Wannan lamarin ya tilasta wa wasu daga cikinsu yin hijira zuwa garin Nguru.

“Sauran yankunan da hamadar ta shafa sun hada da Tulo-Tulo da Bula-tura, garuruwa biyu masu iyaka da Jamhuriyar Nijar.

“Garuruwanmu na fuskantar hadarin bacewa,” in ji Aji.

Shugaban ya bayyana damuwarsa kan cewa nan ba da jimawa hamadar za ta shiga wani tapki mai matukar muhimmanci wajen samar da ruwa a yankin, idan ba a dauki matakan gaggawa na dakile hakan ba.

“ Dunkulewar yashin na barazana ga wani tabki mai ban sha’awa wanda ya ke samar da ruwa don anfanin gida da shuke-shuke musamman lokacin rani

“Wannan haɗari ne a fili kuma ga tattalin arzikin jama’ar mu, ma su noman rake, tumatur, rogo, gyada har ma da dankali.

“Idan aka bar tafkin ya bushe, za a samu matsalar tattalin arziki don mutane za su rasa aikin yi,” in ji shi.

Aji ya bayyana cewa kokarin da karamar Hukumar, gwamnatin jinar, da aikin Great Green Wall na gwamnatin tarayya da ma kungiyoyi masu zaman kansu suka yi ya yi kyau, amma bai samar da sakamakon da ake bukata ba.

Don haka shugaban ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar da wani gandu a yankin domin dakile yashin.

“Ina kira ga ofishin asusun kula da muhalli da gwamnatin tarayya da su ayyana dokar ta-baci kan kwararowar hamada a karamar hukumar Yusufari.

“Muna buƙatar gagarimin shirin dashen itatuwa don hana cigaba da kwarrowar hamadar,” inji shugaban.

Akan shirin karfafa aikin gona na jihar, ya yabawa gwamna Mai Mala Buni, bisa yadda ya ware injinan gona da sauran kayayyakin amfanin gona wa yankin.

“Kayan aiki, taki da ingantattun iri da aka baiwa manoman sun zo akan gaba, lokacin da manoma suka fi bukata.

“ Saboda rarraba kayan gonan a kan kari, za mu girbi amfanin gona mai yawa a wannan shekara, Insha Allahu .

“Saidai mun fuskanci ambaliyar ruwa da zaizayar kasa a bana saboda ruwan sama kamar da bakin kwarya, lamarin da ya kai ga rugujewar gine-gine tare da lalata amfanin gonaki.

“Mun kai tawaga daga gwamnati da SEMA inda gine-ginen suka ruguje, kuma muna sa ran taimako daga gare su nan ba da jimawa ba.(www.nannews.ng)(NAN)
NB/YEN/HMH
============
Mark Longyen ne ya gyara
08032857987

NIHSA, NAN sun hada kai kan wayar da kai kan ambaliyar ruwa, kula da ruwa

NIHSA, NAN sun hada kai kan wayar da kan ambaliyar ruwa, kula da ruwa

 

Ambaliyar ruwa

Daga  Sarafina Christopher

Manajan Darakta / Shugaba, NAN

a Christopher

Abuja, Agusta 27, 2024 (NAN) Hukumar Kula da Ruwan Ruwa ta Najeriya (NIHSA) ta yi kira da a hada hannu da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) don kara wayar da kan al’umma kan albarkatun ruwa da kuma magance ambaliyar ruwa a kasar.

Mista Umar Mohammed, Darakta-Janar na NIHSA ne ya yi wannan bukata yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa Manajan Daraktan NAN, Malam Ali Muhammad Ali, ranar Talata a Abuja.

Mohammed ya ce irin wannan hadin gwiwa yana da matukar muhimmanci idan aka yi la’akari da kalubalen da Najeriya ke fuskanta na ambaliyar ruwa, karancin ruwa da kuma bukatar dawwamammen hanyoyin sarrafa ruwa.

Ya ce NIHSA ce ke da alhakin samar da bayanai kan halin da ake ciki da kuma yadda ake tafiyar da albarkatun ruwa na kasa.

Mohammed ya ce aikin hukumar NIHSA ya hada da bayanai kan wuraren da albarkatun ruwa suke, yawansu, dogaro, inganci da yuwuwar amfani da sarrafa su.

“Wannan yana buƙatar mu ci gaba da samar da ingantaccen ingantaccen bayanai na ruwa da kuma yanayin ruwa.

“Ruwa rayuwa ce amma kogunanmu da tafkunanmu na iya juyowa daga alheri zuwa halaka cikin bugun zuciya.

“Dole ne mu wayar da kan ‘yan kasar mu yadda za su kare kansu da kuma sarrafa albarkatun ruwan mu cikin gaskiya,” in ji shi.

Ya kuma jaddada muhimmancin yin aiki da NAN domin sauke nauyin da ya rataya a wuyan NIHSA da kuma wayar da kan al’umma domin dakile illolin ambaliya.

A nasa martanin, Ali ya taya babban daraktan NIHSA murnar nadin da aka yi masa tare da bayyana shirin NAN na yin hadin gwiwa da NIHSA.

Ya nanata kudurin NAN na yada muhimman bayanai ga jama’a.

“A matsayinmu na babban kamfanin dillancin labarai na kasar, mun fahimci rawar da muke takawa wajen tsara labarai da kuma sanar da ‘yan kasa.”

Ali ya yi karin haske kan yadda NAN ke kai wa, inda ya ce hukumar na da ofisoshi a kasashen Afirka da dama, da suka hada da Afirka ta Kudu, da Cote d’Ivoire, da Addis Ababa.

Manajan daraktan ya kuma yi nuni da cewa NAN na daya daga cikin gidajen labarai guda uku mazauna ginin Majalisar Dinkin Duniya da ke New York.

“Tare da NIHSA, za mu haɓaka al’adar wayar da kan jama’a da ke ba wa al’umma damar yin aikin sake amfani da ruwa tare da daukar matakan da za su magance ambaliyar ruwa.”

Ya ce NAN ta fara yada bayanai cikin harsunan gida.

“Muna da gidan yanar gizon labarai na Hausa kuma kafin shekara ta kare, za mu fadada har zuwa Yarbawa da Igbo; tare da wasu harsunan da za a bi a hankali,” in ji shi. (NAN) (www.nannews.ng)

 

SAF/TAK/CJ/

=========

Tosin Kolade da Chijioke Okoronkwo ne suka gyara

 

 

 

Gwamnatin Tarayya za ta tallafawa jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa da N3bn

Gwamnatin Tarayya za ta tallafawa jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa da N3bn

Tallafi
Daga  Muhammad Lawal
Birnin Kebbi, Agusta. 25, 2024 (NAN) Gwamnatin Tarayya ta ce za ta tallafa wa jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa da Naira biliyan 3 domin dakile illolin da ke tattare da ibtila’in.

Mista Wale Edun, Ministan Kudi Da Gudanar da Tattalin Arziki ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi ranar Lahadi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa ministan ya yi magana ne jim kadan bayan ya duba wasu yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a Kebbi.

Edun ya ce: “A nan zan sanar da cewa Majalisar Tattalin Arziki ta kasa ta himmatu kuma ta dauki matakin tallafa wa daukacin jihohin tarayya da kuma babban birnin tarayya Abuja da Naira biliyan 3 domin rage radadin ambaliyar ruwa a bana.

“Hakan zai sanya Jihohi da yawa kamar Kebbi cikin kyakkyawan yanayi don samun damar shirya manoman su don gudanar da duk wani muhimmin aikin noman rani, wanda muke tsammanin za a samu nasara, da tsare-tsare da kuma aiwatar da su yadda ya kamata.

Hakan a cewarsa, zai kai ga samun nasara, tare da samar da hanyoyin samar da abinci a farashi mai sauki da rage hauhawar farashin kayayyaki da kuma kara daidaita tattalin arzikin kasar.

Ya bayyana aniyar shugaban kasa Bola Tinubu na taimaka musu wajen tabbatar da tsaro, juriya da ingantawa da kara yawan amfanin da suke samu da kuma zama kwandon abinci a Najeriya.

Shima da yake jawabi, Ministan Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sen. Atiku Bagudu, ya koka kan yadda ambaliyar ta shafi kananan hukumomi da dama fiye da yadda ya gani a lokacin da ya ziyarci yankunan kwanan nan.

Sai dai ya yaba da juriya da kwarin gwiwa da mutanen Kebbi suke da shi, inda ya ba da tabbacin za a zaburar da su don yin aiki mai kyau a lokacin noman rani.

Ministan ya ce, baya ga Naira biliyan 3, gwamnatin tarayya ta amince da wani Asusun Renewed Hope Infrastructure Fund wanda za a yi amfani da shi wajen samar da hanyar Badagry zuwa Sokoto da wasu hanyoyin.

“Mafi tsawan doguwar hanyar zai kasance ne a yankin jihar Kebbi. Hakazalika, ban ruwa da madatsun ruwa muhimman fasalin wannan sabon asusun samar da ababen more rayuwan ne.

“Don haka, za a fadada wuraren noman rani a duk fadin titin mai kilomita 1,000 kuma wani muhimmin bangare na tallafin noman zai kasance a Kebbi,” in ji shi.

A nasa bangaren, Gwamna Nasir Idris, ya roki gwamnatin tarayya da ta taimaka wa jihar duba da yadda ambaliyar ruwa ta mamaye filayen noman shinkafa da dama a jihar.

Ya ce: “Sun je Wacot Rice Mill da ke Argungu kuma sun ga abubuwa da kansu. Sun kuma ziyarci Matan Fada a garin Argungu inda suka ga yadda ambaliyar ta shafi gonakin shinkafa.

“Kebbi ita ce kan gaba wajen noman shinkafa a kasar nan, saboda jihar noma ce.”
Gwamnan ya yi kira ga ministocin biyu da su tattauna da shugaban kasar kan yadda za a taimaki jihar Kebbi, inda ya ce jihar na da karfin ciyar da al’umma baki daya da ma sauran su.

A cewarsa, a kokarin da gwamnatin jihar ke yi na bunkasa samar da abinci a kasa, gwamnatin jihar ta raba takin zamani, da itatuwa, famfunan tuka-tuka, da injinan fanfo na CNG ga manoma sama da 35,000 kyauta.

Sai dai ya ce damina ta zo da kalubale da dama, tare da lalata filayen noma.

“Don haka muna son gwamnatin tarayya ta kawo mana agaji domin noman shinkafa ta gabato.

“Tuni mun fara wayar da kan manoman mu cewa nan da nan bayan girbin damina, gwamnati a shirye take ta taimaka musu su koma noman rani,” in ji shi.

NAN ta ruwaito cewa tawagar sun kuma ziyarci cibiyar kula da ruwa ta Dukku a Birnin Kebbi. (NAN)( www.nannews.ng )KLM/MNA
Maureen Atuonwu ta gyara
Nabilu Balarabe ya fassara

Gwamnatin Borno za ta rufe makabartu biyu saboda da cunkoso

Gwamnatin Borno za ta rufe makabartu biyu saboda cunkoso

Makabarta
Daga Nabilu Balarabe
Damaturu, Aug 24, 2024 (NAN) Gwamnatin Jahar Borno ta ce a ranar 1 ga Satumba za ta rufe manyan makabartu biyu da suka cika a Birnin Maiduguri don guje wa barkewar annoba.

Makabartun sun hada da Makabartar Musulmai ta Gwange ta da ke Hanyar Bama da Makabartar Kirista da ke tsohuwar GRA.

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da ke dauke da sa hannun Alhaji Mohammed Abubakar, Babban Sakataren Hukumar Harkokin Addinai ta jihar a ranar Jumma’a a Maiduduguri.

Ya ce gwamnatin ta samar da sabbin makabartu biyu da suka hada da Makabartar Dalori ta kan Hanyar Bama ga Musulmai, da kuma Makabartar alumar Kirista Mai Matsanancin Tsaro da ke kan Hanyar Baga.

Abubakar ya ce samar da sabbin makabartun ya biyo bayan bukatar yin hakan da ga alummai daba daban na jihar.

Babban Sakataren ya kara da cewa gwamnati za ta ci gaba da bude sabbin makabartu a fadin jihar a duk inda akwai bukatar yin hakan.

Ya ce tuni gwamnatin ta sayo motocin guda shida da za ta bayar da su ga alumar Musulmi da na kirista don daukan gawawwaki.(www.nannews.ng)(NAN)NB

Rubutawa: Nabilu Balarabe