NELFUND za ta fadada lamuni zuwa ga dalibai masu horon sana’o’i

 

Lamuni

By Funmilayo Adeyemi

Abuja, Nuwamba 18, 2025 (NAN) Asusun bada lamunu na ilimin Najeriya (NELFUND), ya sanar da shirin tsawaita shirin ba da lamuni na dalibai don shirye shiryen koyon sana’o’i.

Manajan Darakta na NELFUND, Akintunde Sawyerr ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Abuja.

Sawyerr ya ce tsarin fadadawar ya yi dai-dai da shirin gwamnatin tarayya na bunkasa ilimi da fasaha.

Ya kara da cewa matakin ya nuna yadda shugaban kasa Bola Tinubu, ya kuduri aniyar samar da ci gaban jarin masu sana’o’i fiye da ilimin jami’a na gargajiya.

“Babu wata al’umma da masana suka gina su kadai.

“Yana da matukar muhimmanci a sami mutanen da za su iya amfani da hannayensu, a kara masu kuzari, ƙarfafa su, da basira don aiwatar da dabaru masu wayo da ke fitowa daga waɗanda ke fitowa daga cibiyoyin ilimi,” in ji shi.

Sawyerr ya bayyana cewa, yayin da NELFUND ta fi mayar da hankali kan bayar da tallafin kudi ga dalibai a manyan makarantu tun lokacin da aka kaddamar da shi, aka fara shirye-shiryen fadada shi ga masu sana’a da fasaha a fadin kasar.

A cewarsa, mataki na gaba na ci gaban Najeriya yana bukatar daidaito tsakanin kwarewar ilimi da fasaha.

“A NELFUND, muna da hurumin yin sana’o’i.

“Ba mu fara ba tukuna, amma na san cewa gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ta tabbatar da cewa an samu cikakken bayani kan batun.

” Ma’aikatar ci gaban matasa tana yin sana’o’i, ma’aikatar Ilimi ta shiga sana’o’i da kuma ma’aikatar tattalin arziki ta dijital ta shiga cikin dabarun IT.

“Don haka, fasaha wani abu ne da aka sa ma’aikatun gwamnati da yawa da aikatawa.

“Kuma ina ganin a fili yake cewa injiniyan da zai iya yin gini, ya fi injiniyan da zai iya zane kawai.

“Matakin da muke a kasar nan a yanzu, shine abin da zan kira, tsarawa, ginawa, da sarrafa matakin,” in ji shi.

(NAN)( www.nannews.ng )

FAK/ROT

=======

Rotimi Ijikanmi ne ya gyara shi

Aisha Ahmed ta fassara shi.

WAEC/NECO: Wata kungiya ta yi kira da a dakatar da tsarin kayyade shekaru na Gwamnatin Tarayya

WAEC/NECO: Wata kungiya ta yi kira da a dakatar da tsarin kayyade shekaru na Gwamnatin Tarayya

Dakatarwa

Daga Diana Omueza

Abuja, Agusta 29, 2024 (NAN) Wata kungiya mai suna Education Rights Campaign, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dakatar da shekaru 18 da kayyade na daukar jarrabawar kammala jarrabawar Afrika ta yamma (WAEC) da National Examination Council (NECO).

Mista Hassan Soweto, kodinetan kungiyar na kasa ya yi wannan kiran a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Alhamis a Abuja.

NAN ta ruwaito cewa a kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta fitar da wata sabuwar doka da ta kayyade kayyade shekarun ‘yan takarar WAEC da NECO a shekaru 18.

Ministan Ilimi Farfesa Tahir Mamman ya umurci shugabannin hukumar WAEC da NECO na jarrabawar kammala manyan makarantu da su aiwatar da tsarin.

Soweto ya bayyana manufar a matsayin maras buƙata kuma ba dole ba.

A cewarsa, kamata ya yi gwamnati ta dakatar da wannan mataki tare da magance wasu manufofin ilimi da suka shafi dalibai kai tsaye, da kuma harkar ilimi a kasar.

“Maganar ministar tana kokarin tilasta mana mu shiga cikin rigimar da ba ta dace ba maimakon yadda za a yi tsarin ilimi ya yi aiki.

“Mun fahimci bukatar kare ‘ya’yanmu amma wannan manufar wani yunkuri ne na kawar da dalibai da yawa daga samun gurbin karatu mai yiwuwa saboda rashin isasshen sarari a jami’o’i,” in ji shi.

Soweto ya ce tsarin ilimi na 6-3-3-4 da ke da alhakin samar da dalibai daga shekaru 18 da ya kamata su cancanci shiga jami’o’i ya ci tura.

Ya ce hakan na bukatar damuwa ba bullo da wata manufa ba.

Ko’odinetan ya yi kira ga gwamnati da kada ta hukunta daliban da suka nuna bajinta, ta hanyar cin jarabawar WAEC da NECO.

Ya bukaci gwamnati da ta magance matsalolin da suka shafi bunkasar dalibai sau biyu da sau uku zuwa wasu azuzuwan, musamman a makarantu masu zaman kansu da shigar da yara da wuri zuwa makarantun firamare da sakandare.

“Akwai bukatar tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan ci gaban ilimi.

“Manufar ƙayyadaddun shekaru za ta yi kama da horo ga dubban ɗaliban da suka kware sosai kuma suka cancanci shigar da su jami’o’i.

“Dole ne mu dage cewa a dakatar da wannan manufa; Ana kuma buƙatar tattaunawar masu ruwa da tsaki akan duk ma’auni.

“Ya kamata gwamnati ta yi taron kasa don sake duba tsarin 6-3-3-4. A can, masu ruwa da tsaki za su iya ba da gudummawa da sabunta manufofin ilimi na ƙasa.

“Ana kuma sa ran gwamnati za ta magance kalubale kamar rashin tallafin ilimi, yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke yi, rashin ababen more rayuwa, da kuma zubar da kwakwalwa,” in ji Soweto. (NAN)

DOM/CEO/JPE

=========

Chidi Opara/Joseph Edeh ne suka gyara shi